Majalisar Addinin Musulunci a jahar Adamawa ta amice da Atiku Abubakar a matsayin dan takaran da zata zaba a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa ta amice da dan takaran shugaban kasa a jam iyar P D P Alhaji Atiku Abubakar a matsayin wanda zasu zaba a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa. Shugaban majalisar addinin musulunci dake jahar Adamawa Aljahi Gombo Jika ne ya baiyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai karin haske jin kadan da kammala taron majalisar wanda aka gudanar a sakatariyar majalisar dake yola. Alhaji Gambo Jika yace majalisar tayi la akari da yanayin yan takaran inda suka cimma matsaya ganin cewa Alhaji Atiku zasu baiwa kuri arsu domin kasancewarsa dan jahar Adamawa ne wanda kuma suna da yakiinin cewa zai gudanar da aiyukan cigaban kasan nan. Alhaji Jika yace majalisar ta kuma yabawa hukumomin tsaro bisa na mijin kokari da sukeyi wajen daukan dukkanin matakai da sukeyi domin kare rayuka dama dukiyoyin Jama a. Ya kuma jinjinawa gwamnan jahar Adamawa bisa kokari da yakeyi na gudanar da aiyukan cigaban jahar dama inganta t...