Za Kuga Chanji Cikin Kwanaki Dari na farko A Ofis- Zababben Gwamnan Taraba, Agbu
Daga Sani yarima Jalingo. Za Kuga Chanji Cikin Kwanaki Dari na farko A Ofis- Zababben Gwamnan Taraba, Agbu Zababben Gwamnan Jihar Taraba, Kanal Kefas Agbu (mai ritaya) yace da yardan Allah zasu kawo chanji na zahiri cikin kwanaki dari na farko da za suyi a ofis. Agbu ya sanar da hakan ne a lokacin da yake yiwa dunbin magoya bayan Jam'iyyar su ta PDP yawabin godiya jim kadan bayan ya karfi takardan shedan zaben sa daga ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC dake Jalingo. Kwamishinan zabe na hukumar zaben mai zaman kanta ta INEC dake Jihar Taraba, Umar Muktar Gajiram shine ya mikawa zababben Gwamnan Jihar, Kanal Kefas Agbu (mai ritaya) takardan shedan zaben sa a ranar laraba 29 ga watan maris na 2023 da muke ciki. Hakanan kuma, Umar Muktar Gajiram ya mikawa suma zababbun 'Yan Majalisan dokokin jihar ta Taraba guda 24 takardan shedan zaben su a dakin da aka gudanar da tattara sakamakon zaben Gwamnan Jihar wanda ya gudana a ranar 18 ga watan maris din dake cikin h...