Hukumar yan sanda na rike da wani maishekaru 75 da kokarin yiwa yar shekaru 25 fyade a jahar Adamawa.

A yunkurinta na dakile aikata matsalar Fyade a fadin jahar Adamawa rundunan yan sandan jahar tana tsare da wani mutum dan shekaru 75 da haifuwa bisa zarginsa da yunkurin yiwa wata yar shekaru 25 fyade a kauyen Mukuvinyi dake cikin karamar hukumar Hong a jahar Adamawa. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Ngurije ne ya baiyana haka a wata sanarwa da yarabawa manema labarai a yola. Wanda ake zargin mai suna Daniel Jaja yayi kokarin aikata fyaden ne biyo bayan gayyata da yayiwa yarinya zuwa gidansa, wanda kuma hakan yasa ya samu damar ganin zai aikata mata fyade,
Bincike da aka gudanar ya baiyana cewa bai samu damar aikata fyadenba saboda yarinyar tayi amfani da reza wajen jimasa a gabansa, wanda hakan yasa yarinyar ta barshi da rauni wanda a yanzu hakama yana kauce a asibiti domin jinya. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola. yayi Allah wadai da aukuwar lamarin inda ya umurci sashin da ke kula da matsalar iyali da yacigaba da gudanar da bincike kuma da zaran an kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kotu domin ya fuskanci shariya. Kwamishinan yayi anfani da wannan dama wajen kiran daukacin al umma jahar musammanma wadanda ke zaune a kauyuka da sukasance suna taimakawa rundunan da wasu bayanai da zasu taimaka wajen dakile aikata lafuka a tsakanin al umma.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.