Mutane 15 da ake zargi da aikata laifuka sun shiga hanun Yan sanda a jahar Adamawa.

 



Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankombo Morris ya yabawa Al ummar jahar Adamawa bisa kokari da sukeyi na baiwa rundunan yan sanda hadin Kai da goyon baya wajen yaki da ta addanci a fadin jahar.



Kwamishinan yace yanzu hakama rundunan ta samu nasaran damke mutane 15 da ake zargi da  aikata laifuka a bayan gudanar da bikin Sallah a tsakanin Yola da Jimeta.




Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.



Sanarwan ta baiyana cewa an gano makamai masu hatsari da miyagun kwayoyi, wayoyi da sauransu a wurin wadanda ake zargi.



A cikin sanarwan an jiyo kwamishinan yan sandan ya tabbatar da cewa da zaran an kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu domin su fuskanci shariya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.