An kirayi shuwagabani a Najeriya da su gudanar da bincike kan kisan da akayiwa mafarauta a jahar Edo.













Kwamandan Kungiyar mafarauta ta kasa a Najeriya Alhaji Muhammed Adamu ne yayi wannan kira a sakonsa na jaje da ya rabawa manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.




Alhaji Muhammed Adamu ya shawarci shuwagabanin Najeriya da suyi dukkanin Mai yiwa domin gudanar da cikekken bincike dangane da kisan mafarautan Arewacin Najeriya da Kayi a jahar Edo tare da hukunta duk Wanda aka samu da hanu a cikin kisan.




Alhaji Adamu ya shawarci mafarautan dake fadin Najeriya da sukasance masu Kai zuciya nesa tare da kaucewa duk abinda zai haifar da tashin hankali da Kuma su guji daukan doka a hanu domin kawo yanzu ana cigaba da gudanar da bincike dangane da lamarin.




Ya Kuma jajantawa iyalen wadanda suka rasa rayukansu tare da yin adu a ga Allah madaukakin sarki da ya gafarta musu ya Kuma Aljanna Firdausi ce makinarsu.




Alhaji Adamu ya Yi ad ar Allah madaukakin sarki ya kare Najeriya da shuwagabanin ta ya Kuma kare mafarauta a duk inda suke, yace da yardan Allah zasu gacewa anyi adalci dangane da lamarin domin Samar da zaman lafiya dama cigaban kasar baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie