A karon farko an yaye dalube da suka kammala sakandaren a Nasarawo.
Makarantar Sakandaren Nasarawa tayi bikin yaye dalubenta karon farko, bikin ya gudanane a harabar makarantar dake Nasarawo cikin garin jimeta a karamar hukumar Yola ta arewa.
Da yake jawabi a wurin bikin Sakataren Zantarwan hukumar dake kula da makarantun gaba da Firamare a jahar Adamawa Mr Birsan Penuel ya yabawa makarantar bisa shirya wannan biki Wanda yace yin haka yana da muhimmanci domin zai karawa dalube kwarin gwiwa cigaba da karatunsu yadda ya kamata.
Mr Birsan ya Kuma tabbatar da cewa hukumar zatagi dukkanin maiyiwa domin inganta karatu dama ilimin dalube dake fadin jahar Adamawa, don haka ne ma ya gargadi malamai da su Maida hankalinsu wajen aikinsu indama yace duk malamin da aka samu yana sakaci da aikinsa tafa zai fuskanci hukumci.
Mr Penuel ya shawarci iyaye da Suma su bada tasu gudumawa wajen Maida hankalin kan karatun yaransu domin ganin yaran sun samu inganceccen karatu yadda ya kamata.
Ya Kuma kirayi shuwagabanin makarantun gaba da Sakandaren dake fadin jahar da sakasace suna sanya ido kan malamai a Koda yaushe domin ganin komai ya tafi yadda ya kamata ba tare da matsalaba.
Ya yabawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa kokarinsa na Maida hankali kan bangaren ilimi dake fadin jahar.
Shima a jawabinsa Muhammed Usman yace wannan shine karon farko da aka yaye dalube a makarantar tundra aka kafata, saboda suna iya kokarinsu domin ganin an baiwa daluben nagartanccen ilimi domin samun cigaban.
Shima ya kirayi iyaye da sukasance suna baiwa malamai hadin Kai da goyon baya domin ganin an samu nasaran inganta ilimi a tsakanin daluben yadda ya kamata.
Shima shugaban makarantar ta sakandaren Nasarawa malam Yohana Godfrey ya baiyana cewa karon farko an yaye dalube sama da tamanin wadanda suka rubuta jarabawan Karshen na kammala sakadare.
Yace sun shirya bikin ne domin karawa dalube deke biye kwarin gwiwa domin ganin Suma suyi abun Azo agani.
Wasu daga cikin dalube da aka yaye sun baiyana farin cikinsu tare da jindadinsu biyo bayan kammala makarantarsu inda sukace sasuyi amfani da abinda suka Koya domin cigaban ilimi a fadin jahar.
Comments
Post a Comment