An baiyana muhimmanci illimin ya' mace.
An bukaci da a baiwa mata ilimi domin ilimin mata yana da matukan muhimmanci a tsakanin Al ummah.
Shuwagabanin mata ne suka baiyana haka a zantawarau da jaridar An Nur Hausa a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Hajiya Rukaiyya itace mayaimakiyar ahugabar kwamitin women in Da awa a jahar Adamawa, tace illimin ya' mace abune da yake da tasiri sosai a tsakanin jama a, domin a cewarta da zaran ya' mace ta samu illimin to iyali ma gaba Daya sun samu illimin.
Hajiya Rukaiyya ta Kara da cewa illimin mata yana bada gudumawa sosai wajen Gina iyali saboda Ashe bai kamata ace anyi wasa ko watsi da illimin mataba, saboda haka tana kira da babban murya ga iyaye, masu ruwa da tsaki da su Maida hankali wajen baiwa mata ilimi.
Ta Kuma kirayi matan da sukasance masu Maida hankali wajen Neman illim da ma sana o I da zasu dogara da kansu domin inganta rayuwarsu yadda ya kamata.
Itama anata bangaren Hajiya Fadimatu Marafa tace ilimin ya' mace yana da matukan muhimmanci domin a cewarta a kwai banbanci sosai a tsakanin macen da take da illimi da Wanda Bata da illimi, a wajen zaman takewa da ma kula da iyali.
Saboda haka a kwai bukatan Maida hankali wajen baiwa mata ilimi domin hakan zai basu damar kula da iyalinsu yadda yakamata da Kuma mu Amala da jama a ba tare da matsalaba.
Hajiya Fadimatu ta baiyana cewa illim ya' mace ne zai jagoranceta wajen koyon sana o I da zata taimakawa iyalinta dama sauran Al umma.
Ta Kuma shawarci mata da sukasance masu biyayya a Koda yaushe da Kuma tausayawa domin a cewarta hakan zai basu damar inganta rayuwarsu Dana iyalensu baki Daya.
Comments
Post a Comment