An shawarci Al umma Musulmai kan jadin Kai da zaman lafiya.
An shawarci Al umma Musulmai a fadin Najeriya da suyi amfani da lakacin bukukuwar Babban sallah wajen yin dukkanin abinda suka dace domin samun jadin Kai da zaman lafiya a tsakanin Al umma baki Daya.
Kwamishin kananan da matsa gatar sana o I a jahar Adamawa Alhaji HammanJumba Gatugel ne ya bada wannan sahawara a wata sanarwa da ya fitar dangane da bikin Babban sallah a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Alhaji HammaJumba Gatugel yace lokacin bukukuwar sallah lolacine da yake da muhimmanci ga Al umma Musulmai, don haka ya kamata Al umma Musulmai suyi amfani da wannan lokacin domin Jada Kai Mai daurewa.
Alhaji HammanJumba ya kirayi malamai musamman masu gabatar da wa azuzzuka dama huduba da su Sanarwa Al umma Musulmai mahimmancin zaman lafiya dama hadin Kai.
Ya Kuma kirayi Al umma Musulmai da su Kara azama wajen adu o I domin neman taimakom Allah madaukakin sarki wajen kawo Karshen dukkanin kalubalen tsaro a jahar dama kasa baki Daya.
Ya Kuma jaddada yabonsa ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa aiyukan cigaba da take gudanarwa a fadin jahar Adamawa. Tare da tayashi murnan bikin sallah tare da yi masa adu ar Allah ya taimakeahi ya samu nasaran cigaba da aiyukan cigaban jahar ta Adamawa.
Comments
Post a Comment