An shawarci manoma su rinka tuntuban manasan akan harkokin noma.
A yayinda da aka shiga yanagin damina an shawarci manoma da sukasance masu tuntuban masana harkokin noma a Koda yaushe domin bunkasa harkokin nomansu yadda ya kamata.
Masani kan harkokin noma a jahar Adamawa Usman Suleiman Palam ne yayi wannan kira a zantarwarsa da manema labarai a Yola.
Usman Suleiman Palam yace tuntuban masana a harkokin noma abune da yake da matukan muhimmanci saboda haka duk Wanda yakeso ya bunkasa harkokinsa na noma da ya Maida hankali wajen tuntuban masana akan lokacin domin magance matsalar gonarsa.
Usman ya Kara da cewa idan manomi ya kasance yana tuntuban masana a Koda yaushe to yana da wuya yayi asaran nomansa domin zai samu cigaba sosai.
Palam ya jaddada kiransa ga manoma da cewa da zaran manomi ya ga abinda bai ganeba a gonarsa da ya gaggauta garzayawa wajen masana domin daukan matakin gaggawa a wani matakin na dakile matsalar gonarsa.
Suleiman ya Kuma kirayi manoman da sukasance masu hada kansu da Kuma kaucewa duk abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin manoma da makiyaya, domin bunkasa harkokin noma da tattalim arziki a jahar dama kasa baki Daya.
Ya kirayi dukkanin masu ruwa da tsaki a harkokin noma da su taimakwa manoman da kayakin aiki dama shawarwari da zai taimaka musu wajen gudanar da aiyukansu.
Da wannan ne ya kirayi daukacin matasa da suma su shiga a dama dasu a harkokin noma domin Samar da aikin Yi a tsakanin matasan domin Samar da zaman lafiya dama cigaban kasa baki Daya.
Comments
Post a Comment