Karon farko an bude cibiyar sayar da iskar gas wato CNG a yankin Arewa masu gabas
Gwamnan Jihar Adamawa, Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri, wanda Mataimakiyar Gwamna, Farfesa Kaletapwa George Farauta ta wakilta, ta halarci bikin kaddamar da cibiyar iskar gas ta farko a Arewa maso Gabas (LCNG Hub) tare da Karamin Ministan Man Fetur (Gas), Rt. Hon. Ekperikpe Ekpo, PhD, a Yola.
An gudanar da bikin a Filin Jirgin Sama kasa da kasa na Lamido Aliyu Mustapha, wanda ya nuna wani mataki ne mai muhimmanci wajen wanzar da makamashi mai dorewa da bunkasa tattalin arziki a yankin.
Wannan Cibiyar LCNG, hadin gwiwa ne a tsakanin kamfanin Greenville LNG da Gwamnatin Tarayya ta Najeriya, wadda za ta sauya tsarin rarraba makamashi ta hanyar kai iskar gas mai ruwa (LNG) da iskar gas da aka matse (CNG) zuwa yankuna masu nisa ta hanyar "virtual pipelines".
Wurin zai kuma zama tashar cika man iskar gas ga motocin da ke amfani da gas, wanda hakan zai rage kudin sufuri da kuma bunkasa zirga-zirgar ababen hawa masu tsafta.
A jawabin ta na musamman, Mataimakiyar Gwamna jahar Adamawa Farauta ta jaddada kudirin jihar Adamawa na tallafawa shirye-shiryen makamashi da ke kara habaka tattalin arziki da kuma kare muhalli. "Wannan cibiya za ta canza harka wajen samar da masana’antu da bunkasar tattalin arziki da kowa ke da rabo a ciki," in ji ta, tana nuni da irin tasirin da zata yi ga al’umma.
Minista Ekpo ya yabawa aikin da cewa ginshiki ne na ajandar "Shekarar Gas" ta Najeriya, inda ya jaddada muhimmancinsa wajen amfani da dimbin arzikin iskar gas na kasar domin karfafa tattalin arziki da samun isasshen makamashi. "Wannan wata fitila ce ta fata, wadda ke tabbatar da cewa kowa na da damar samun makamashi a Najeriya," in ji shi.
Taron ya samu halartar mutane daban-daban ciki har da mambobin Majalisar Zartaswa ta Jihar Adamawa, sarakunan gargajiya, kwararru daga bangaren makamashi da sufuri, da kuma wakilan kungiyoyin masu sana’ar Keke Bajaj da Keke TVS, wanda ke nuna irin goyon bayan da aikin ke samu.
Ana sa ran wannan cibiya za ta samar da ayyukan yi, karfafa ‘yan kasuwa na cikin gida, da kuma janyo jari a fannin makamashi mai tsafta, wanda hakan zai kara darajar Adamawa a matsayin jagora a fannin makamashi a yankin Arewa maso Gabas. Haka kuma, ya dace da burin Najeriya na kare muhalli ta hanyar rage hayaki da kuma wanzar da ci gaban da ke dauke da sauki ga muhalli.
Wannan muhimmin aiki alama ce ta sabuwar makoma ta makamashi mai dorewa a Adamawa da Najeriya gaba É—aya, wanda ke zama abin koyi na kirkire-kirkire da ci gaban da ke dauke kowa da kowa a gaba.
Comments
Post a Comment