Mahauta Sangere sunyi Kiran Samar musu da kwata.
Mahauta dake Sangere cikin karamar hukumar Yola ta kudu sun kirayi gwamnatin jahar Adamawa da tayi dukkanin abinda suka dace domin gina musu kwata domin samun saukin gudanar da aiyukansu yadda ya kamata.
Mahauta sunyi wannan kirane a zantawarau da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Mallam Isiyaku Abdullahi wakilin sarkin Fawan Namtari Kuma sarkin Fawan sangere yace ya zama dole su kirayi gwamnatin duba da yadda mahauta sama da dari suna gudanar da aiyukansu a Sanger amman basu da wadaceccen kwata Wanda a yanzu haka ma sai sunyi amfani da filin haya wànda Kuma hakan ya na haifar musu da cikas a harkokinsu na Fawa a Sangere.
Saboda haka suna rokon gwamna Ahmadu Umaru Fintiri kasancewa Mai fada ya cika ne ya taimaka ya gyara musu kwata Wanda hakan zaitaimaka wajen cigaba a yankin Namtari baki Daya.
Isiyaku Abdullahi ya yabawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa kokarinsa na gudanar da aiyukan cigaba da ma inganta tsaro, bunkasa ilimi da dai sauransu a fadin jahar.
Isiyaku ya Kuma baiyana cewa suna biyan gwamnatin kudaden haraji saboda da haka ya kamata gwamnati tayi la akari dasu domin Samar musu da kwata.
Shugaban mahauta a Sangere Mallam Kabiru Abubakar yace Samar da kwata a yankin zaitaimaka wajen inganta aiyukansu dama bunkasa kasuwancinsu a yankin harma da cigaba yadda ya kamata.
Kabiru Abubakar ya Kuma dukkanin masu ruwa da tsaki da su taimaka wajen Samar musu da kwata domin inganta aiyukansu, harma da wanzar da zaman lafiya a yankin na Namtari.
Shikuwa Musa Adamu Kiran gwamnatin yayi da ta Samar musu da cibiyar kiwon lafiya a yanki domin samun saukin gudanar da rayuwarsu yadda ya kamata.
Comments
Post a Comment