AN BUKACI AL UMMA MUSULMAI DA SUYI AMFANIN DA KWANAKI GOMA NA KARSHEN RAMADAN WAJEN YIN ADU O I SAMAR DA ZAMAN LAFIYA.

 






Daga Alhassan Haladu Yola.


A yayinda aka shiga kwanaki goma na karshen watan Azumin Ramadan am kirayi Al umma musulmai a fadin Najeriya da su Kara himma wajen yin ibada da Kuma yiwa kasa da shuwagabanin adu o I domin Samar da zaman lafiya da ma cigaban kasa baki Daya.



Shugaban majalisar harkokin addinin musulunci a jahar Adamawa Mallam  Gambo Jika ne yayi wannan Kira a zantawarsa da manema labarai a Yola.



Mallam Gambo Jika yace kwanaki goma na karshen Ramadan suna da matukan muhimmanci ga Al umma musulmai don haka ya Kamata Al umma musulmai sukasance masu rubbaiya ibadansu da Adu o I domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo dukkanin kalu balen tsaro dama tsadar rayuwa a fadin Najeriya baki Daya.



Gambo Jika ya kirayi malamai musammanma masu gudanar da tafsirin Azumin watan Ramadan da su fadakar da muhimmanci zaman lafiya da Adu o I da hadin Kai domin Samun cigaba.



Gambo ya Kara da cewa akwai bukatan Al umma musulmai musammanma masu hanu da shuni sukasance suna taimakawa marassa galihu, marayu domin Samun falala dama cigaban dukiyarsu.



Jika yaja hankalin iyaye da suyi amfani da wannan lokaci na Ramadan wajen yiwa yaransu Adu o I domin inganta rayuwarsu yadda ya Kamata.


Ya Kuma jaddada aniyar majalisar na yin dukkanin abinda suka dace domin Samar da hadin Kai da cigaban addinin musulunci yadda ya Kamata.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie