DAGA CIKIN BIKIN RANAN YAN SANDA. RUNDUNAN TA SHIRYA TATTAKI NA MUSAMMAN KAN ZAMAN LAFIYA.
Daga Alhassan Haladu Yola.
yayinda ake ranan Yan sanda ta kasa rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta gudanar da tattalin daga shelkwayan Yan sanda inda akabi kantitin Muhammed Mustafa zuwa titin Olisegun Obasanjo Wanda Kuma an kitse tattakin a shelkwatar rundunan dake Yola.
Tattakin ya hada dukkanin manyan da kananan jami an Yan sanda karakashin jagorancin kwamishinan Yan sanda jahar Adamawa Kabiru Umara Hassan Kuma an gudanar da tattakin cikin kwanciyar hankali ba tare da matsalaba.
An dai oammala tattakin ne a shelkwatar rundunan Yan sandan dake Yola. Da yake yiwa jami an Yan sandan jawabi kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Kabir Umar Hassan ya baiyana farin cikinsa dangane da yadda jami an Yan sandan suka Bada hadin Kai a lokacin tattakin tare da tabbatar musu da cewa zaiyi dukkanin abinda suka dace domin ganin an Samu cigaba yadda ya Kamata.
Kwamishinan ya Kuma jaddada aniyar rundunan na kare rayuka da ma dukiyiyin Al umma da wannan nema yake Kira ga daukacin Al umma da su taimakawa rundunan Yan sanda da wasu baya nai da zasu taimaka wajen dakile aikata laifuka a tsakanin Al umma.
Wasu daga cikin kungiyoyi da suka bi tattakin sun baiyana farin cikinsu da godiyarsu dangane da wannan tattakin da rundunan Yan sandan ta shirya.

Comments
Post a Comment