Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta fara tantance masu aniyar shiga Yan sanda.

 




Daga Alhassan Haladu Yola.


Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta fara tantance masu aniyar shiga aikin Yan sandan wadanda ake kokarin diba a kwanan Nan, an fara gudanar da tantancewar ne a makarantar yaran Yan sanda dake barikin Yan sanda a karewa dake  cikin garin Jimeta.




Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da kakakin Rundunan Yan sanda jahar SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya wallafa a ahafinsa na sada zumunta.





Sanarwan ta baiyana cewa shugaban sashin diban Yan sandan DCP Musa Bulus tare da shugaban tawagan Hukumar kula da harkokin Yan sanda Alhaji Bappai Abdullahi Suleiman da suke yiwa jami an da zasu gudanar da tantancewar    jawabi sun kirayesu da su gudanar da aiyukansu bilhakki da gaskiya domin ganin an tantancesu cikin tsanaki ba tare da wata matsalaba.




Sanarwan tana mai sanar da wadanda ke Neman aikin Yan sanda da cewa ana gudanar da tantancewar ne kyauta tare da gargadin kaucewa duk abinda zai Karya doka domin tantancea ya gudana cikin lumana.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie