Shugaban UBRBDA ya baiyana aninyarsa na faddada ban ruwa a Geriyo domin Samar da wadaceccen abinci. a jahar Adamawa.



By Ibrahim Abubakar Yola.


Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Upper Benue River Basin Development Authority (UBRBDA), Amb. Dr. Mahmud Sanusi Mohammed, ya jagoranci mambobin kungiyar wakilain kafafen yada labarai dake Yola a  Jihar Adamawa zuwa rangadin duba aikin ban-ruwa na Lake Geriyo Irrigation Project da ke Yola.



Ziyarar ta bai wa ‘yan jarida damar ganin matakin shirye-shiryen da aka kammala domin fara kakar noman rani ta shekarar 2025/2026, bayan wasu muhimman gyare-gyare da ayyukan fasaha da Hukumar ta aiwatar domin inganta tsarin ban-ruwan.



Da yake jawabi ga manema labarai yayin rangadin, Dr. Mahmud Sanusi Mohammed ya jaddada muhimmancin noman ban-ruwa wajen tabbatar da wadatar abinci a Najeriya.



Ya bayyana cewa ayyukan da ake gudanarwa a Geriyo suna daidai da manufofin gwamnatin tarayya karkashin Renewed Hope Agenda na Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na karfafa Samar da abinci da bunkasa noma a kasa.



A cewarsa, Hukumar ta gudanar da aikin cire laka da yashi a wasu muhimman sassan Kogin Benue, tare da tsabtace manyan da kananan magudanan ruwa na ban-ruwa da kuma cire ciyayi masu hana ruwa gudana domin inganta shigar ruwa cikin tsarin ban-ruwan.



Haka kuma, shugaban Hukumar ya nuna sabbin injinan famfon ruwa da aka girka a aikin, wadanda za su taimaka wajen inganta yadda ake debo ruwa da rarraba shi ga manoman da ke anfani da shirin ban-ruwan


.

Bugu da kari, Hukumar ta gyara hanyar shiga Geriyo ta hanyar amfani da sabuwar fasahar biotechnology, wadda ke rage sharar gini tare da kare muhalli.



Dr. Mohammed ya bayyana gamsuwarsa da ci gaban da aka samu, yana mai cewa hadin gwiwar wadannan ayyuka – gyaran hanyar kogin, tsabtace magudanan ruwa, cire ciyayi masu hana ruwa gudana, girka sabbin injinan famfo da kuma gyaran hanya – sun kara inganta aikin ban-ruwan na Geriyo domin fara kakar noman rani cikin nasara.



A nasa bangaren, mambobin Correspondents Chapel sun yabawa wannan shiri, inda suka ce ziyarar ta ba su damar ganin kai tsaye irin ci gaban da aka samu da kuma kokarin Hukumar wajen farfado da ayyukan ban-ruwa domin tallafawa tsaron abinci a Najeriya.



Tawagar da ta raka MD/CEO yayin ziyarar ta hada da Babban Mataimaki na Fasaha ga MD, Manajan Workshop, Manajan Aikin Ban-Ruwa na Geriyo da sauran ma’aikatan fasaha na Hukumar.



Hukumar Upper Benue River Basin Development Authority ta sake jaddada kudurinta na kara bunkasa ayyukan ban-ruwa, inganta sarrafa albarkatun ruwa da kuma tallafawa noman da ake yi duk shekara a yankin Kogin Benue.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins