DUBBAN MASU ZABE NA KARKARA DAKE ADAMAWA NA CIKIN HATSARIN RASA ZABEN 2027
By Bamanga Abdullahi Gombi Yola.
Dubban masu zabe na al'ummomin karkara a fadin Jihar Adamawa na cikin hatsarin rasa halartar babban zaben 2027, saboda rashin isasshen wayar musu da kai akan rajista da karban katin zabe na dindindin.
Binciken da Radio Nigeria ta gudanar ya gano cewa rashin wayar da kan jama'a da kuma karancin cibiyoyin rajista da karban katunan zabe ne zasu hana masu sauke wannan hakki nasu.
Wani mazaunin Kauyen Koda dake Karamar Hukumar Girei mai shekara 30, Abubakar Maigari, ya bayyana damuwarsa kan wahalar samun katin zabe na dindindin a yankinsu.
Ya ce duk da cewa ya yi rajista a baya, amma bai samu damar karban katin ba saboda rashin cikakkiyar bayani.
Maigari ya ce rashin cibiyar yanka da karban katin zabe a Koda yana tilasta wa mazauna zuwa Girei, kuma tsadar kudin mota na hana mutane da yawa zuwa karban katunan su.
"Matan aure da dama basuje suka Karbi katunan su ba, saboda ko rashin kudin mota, kokuma mazansu basu yarde musu da hanyaba."
Haka zalika, wani mazaunin Kauyen Gudumniya dake Karamar Hukumar Hong mai shekara 18, Hamidu Bamanga, ya ce bai yi rajistar ba saboda halin wasu 'yan siyasa, na yin son ransu ne kawai bayan zabe, lamarin da ya sa shakku ga matasa da dama, wadanda ke ganin shugabannin da aka zaba ba sa damuwa da bukatun jama'a, musamman matasa.
"Karban katin zabe ne kawoi zai bawa matasa damar kalubalantan Shugabanni da zaban Adilai a kan Mulki."
A halin yanzu, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta "INEC" a Jihar Adamawa ta ce masu kada kuriya da dama basu Karbi katunan su ba, duk da kokarin da hukumar tayi na raba wuraren karban a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.
Jami'in Hulda da Jama'a na Hukumar na Jihar, Dahiru B. Jauro, ya ce an kafa cibiyoyin rajista bisa tsarin sauya su a matakin unguwa, musamman a yankunan da ke da wahalar shiga, domin sauwaka wa jama'a rajista da karban katin su
“Ana cigaba da bada katin zabe Kashi na uku, Wanda aka fara ranar 11 ga watan Mayu, da farko an shirya kammala shi ran 10th July, amma daga baya an Kara sati biyu."
Ya yi kira ga dukkan 'yan Najeriya masu shekara 18 zuwa sama, da kuma wadanda ke da matsala a katunan su, da su yi amfani da wannan karin lokaci wajen yin rajista da tattara katunan su.
A nasa jawabi, Shugaban Radio Najeriya, Fombina FM Yola, Alhaji Muhammad Babayo Asha, ya ce tashar na ci gaba da habaka rajistar masu zabe da karban katin su, ta hanyar shirin siyasa mai suna "Nigeria A Yau", da kuma wasu shirye-shirye da ake watsa su cikin harsunan gida domin wayar da kan al'ummomin karkara.
"Ya jaddada aniyar gidan Radiyon wojen cigaba da ilmantar da masu kada kuriya tawojen shirye shirye akan zabe da ingantattun labarai."
Darektan Hukumar Wayar da Kan Jama'a ta Kasa "NOA" na Jihar Adamawa, Richard Bala Dangari, ya ce Hukumar na kara kuzari wajen wayar da kan jama'a a kananan hukumomi 21 na jihar ta hanyar sarakunan gargajiya, shugabannin addini, da jami'an wayar da kan jama'a da ke magana da harsunan yankin.
Dangari ya ce "NOA" na hada kai da kafafen yada labarai da jam'iyyun siyasa domin inganta harkar Regista da karban katin zabe na dindindin a fadin jihar.
Darektan ya kuma bayyana tattara cibiyoyin rajista a hedkwatar kananan hukumomi, cunkoso, wahalar tattalin arziki, da rashin amincewar jama'a da tsarin zabe a matsayin manyan cikas, inda ya kara da cewa Hukumar na aiki wajen maido da kwarin guiwar jama'a kan tsarin zabe da kuma karfafa dimokuradiya.

Comments
Post a Comment