BIKIN MAULIDI AN KIRAYI MALAMAI SU MAIDA HANKALIN KAN HADIN KAI DA ZAMAN LAFIAY.
Daga Alhassan Haladu Yola.
An shawarci malamai musamman ma masu gabatar da nasihu a wuraren bukukuwar mailidi da sukasance masu gudanar da nasiha kan hadin Kai da zaman lafiya domin Samun cigaban zaman lafiya mai daurewa.
Sheikh Muhammadu Modibbo Jingi sarkin yaki. ne ya Bada wannan shawara a zantawarsa da manema labarai dangane da shigowar watan Mailidi.
Sheirk Muhammadu Modibbo yace wannan wata ma maulidi Yana da falala mai yawa saboda haka akwai bukatar Al umma musulmai su Kara himma wajen yin Adu o I harma da gudanar da aiyukan Alheri domin Samun dubbin Lada daga Allah madaukakin sarki.
Shehin Malamin ya kirayi Al umma musulmai da su Kara kaimi wajen Nuna soyayya da kaunar manzon Allah ya zukatansu Wanda hakan zai taimaka wajen inganta rayuwar Al umma musulmai dama cigaban addinin musulunci yadda ya Kamata.
Sheikh Modibbo ya Kuma Kara da cewa akwai bukatar Al umma musulmai su zage damtse wajen yin inadu da Kuma koyi da halayen mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi domin Samun tsira ranan gobe kiyama.
Modibbo yace ya Kamata a dukufa wajen yin Adu o I da aikata Alheri dama sadaka domin a cewarsa hakan zai taimaka wajen cigaban addinin musulunci harma da wanzar da zaman lafiya mai daurewa.
Sheikh Jingi ya Kuma baiyana cewa a wannan watan ne aka baiyanar da monzon don haka Yana da matukan muhimmanci a cigaba da koyi da halayensa da Kuma bin karantarwarsa domin Samun cigaba.
Malamin ya shawarci matasa da sukasan masu gudanar da bukukuwar maulidi bisa tsari da bin doka su Kuma kaucewa duk abinda zai kawo tashin hankali ko rarrabuwar Kai a tsakanin Al umma.
Dangane da matsalar tsaro da tattalin arziki kuwa Sheikh Jingi ya kirayi daukacin Al umma musulmai da su Kara kaimi wajen yin Adu o in wanzar da zaman lafiya da Kuma kawo karshen matsalar tsaro Dana tattalun arziki a fadin Najeriya.
Don haka nema yake Kira ga malamai masu gabatar da jawabi a wuraren bukukuwar maulidi da sukasance suna gudanar da Adu o I na musamman domin Neman taimakon Allah ma daukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubale tsaro a fadin Najeriya.

Comments
Post a Comment