Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta tura jami anta domin ganin an sake zabuka lafiya.

Rundunan yan sandan jahar Adamawa tace ta kimtsa tsaf domin ganin an kammala zabe da za sake a wasu mazabu dake fadin jahar Adamawa. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Sanarwa tace rundunan ta hada kai da takwarorinta domin daukan dukkanin matakai da suka dace domin ganin ba a samu tashin hankaliba a lokaci dama bayan zabe. Sanarwan ta kima kirayi all ummah jahar ta Adamawa da sukasance masu kai rahoton dukkanin abinda basu yarda da shiba tare kuma da baiwa hukumomin tsaro hadin kai da goyon baya domin ganin an kammal zaben lafiya. Harwayau sanarwa ta kara da cewa rundunan zata saka kafar wando daya da dukkanin wanda zaiyiwa doka karan tsaye. Don haka ya kamata a kaicewa duk abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin al umma.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE