An shawarci Al umma musulmai da suyi amfani da wannan lokaci na bukukuwar Maulidi wajen yiwa kasa Adu a.

yayinda ake cigaba da bukukuwar maulidi domin tunawa da ranan haifuwar mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbatar agareshi. An shawarci malamai masu gudanar da jawabai dama nasihohi a wuraren bukukuwan bikin na maulidi da su maida hankali wajen yin dukkanin abinda zai kawo hadin kai da zaman lafiya a tsakanin Al umma. Shugaban Annahada International Islamic Organization shiyar jahar Adamawa Sheik Modibbo Aliyu Wuro Yobbe ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a Yola. Sheik Modibbo yace ana gudanar da bukukuwar maulidinne domin tunatar da Al umma musulmai halayen manzon Allah da Kuma tarihinsa dangane da rayuwarsa da Kuma yadda ya zauna da jama a daban daban. Don haka ya kamata Al umma musulmai suyi koyi da halayen manzon Allah a Koda yaushe domin ganin an samu zaman lafiya a tsakanin Al umma. Modibbo Aliyu ya Kuma ja hankalin mahalarta bukukuwar Maulidi da sukasance suna amfani da abimda sukaji a wurin bukukuwar na maulidi Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen samun hadin Kai harma da Samar da zaman lafiya Mai daurewa a tsakanin Al umma baki Daya. Ya kara da cewa kawo yanzu ana samu cigaba sosai wajen hadinkai dama zaman lafiya duk da cewa kasar na fama da matsalar tsaro. Da wannan nema yake kira ga malamai dama mahalarta bukukuwar maulidi da suyi amfani da wannan lokaci wajen yiwa kasa Adu o i domin Neman taimakon Allah ma daukakin sarki wajen kawo dukkanin kalubalen tsaro da keciwa kasar tuwo a kwarya. Ya Kuma yi fatan gani an kammala bukukuwar Maulidi a fadin duniya lafiya ba tare da samun matsalaba.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE