An yaba da kamun ludayin Shugaba Bola Tinubu cikin kwanaki dari dayayi akan mulki.

A yayinda shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya cika kwanaki dari akan Mulki shugabancin Najeriya an yaba da kamun ludayinsa duba da irin yanayin matsalar rayuwa da ake ciki. Alhaji Adam Hassan Ibrahim shugaban kungiyar yan kasuwa a Arewacin Najeriya ne ya baiyana haka a zantawarsa da jaridar Al Nur bayan godiya da yayiwa Allah madaukakin sarki yace shugaba Bola Tinubu ya taka rawan gani a fannoni daban daban a cikin kwanaki dari da yayi na farkon mulkinsa. Alhaji Adam Hassan yace shugaba Bola Tinubu ya fitar da tsare tsare da zasu kawo cigaban kasa musammanma a bangaren tattalin arziki da Kuma bunkasa harkokin noma da dai sauransu. Alhaji Hassan yace duk dacewa ana cikin wani yanayi da wahalar rayuwa Amman da yardan Allah komai zai daidaita domin kuwa a cewarsa bayan wahala akwai sauki. Ya kara dacewa ko a yanzu hakama shugaban kasa ya tafi kasar indiya domin halartan taron G 20 domin ganin Najeriya ta zuna jari wajen harkokin kasuwanci kasa da kasa. Wanda Kuma hakan Yana daga cikin abinda ke kawo cigaba a kasa. Saboda haka kwanaki dari da shugaba Tinubu yayi, yayi kokari sosai. Dangane da tsaro kuwa Bola Tinubu yayi kokari don ya inganta fannin tsaro Wanda Kuma da yardan Allah za a kawo karshen matsalar baki Daya. Saboda yaka ya kamata yan Najeriya mucigaba dayin adu o I domin Neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen kalubalen tsaro a fadin Najeriya baki Daya. Yace tun daga lokacinda shugaba Tinubu ya karbi rantsuwar kama mulki a ranan 29-5-2023 ya kawo abubuwan cigaba da Kuma fitar da tsaren cigaban kasan nan baki Daya. Don haka nema yake kira ga daukacin yan Najeriya da sukasance masu hada kansu da kuma baiwa gwamnatin hadin Kai da goyon baya domin ganin ta cimma burinta na bunkasa tattalin Arzikin kasa baki Daya. Harwayau Alhaji Hassan yace duk da cewa kwanaki dari yayi kadan ace za a auna yanayin kamun ludayin shugaba Tinubu Amma. Kwanaki dari suna da muhimmanci ga shugaba don haka Al umma sukasance masu hakuri a Koda yaushe nan bada dadewaba komai zasu daidaita. Alhaji Adam Hassan Ibrahim ya taya shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shetima murnan cika kwanaki dari akan Mulki tare da Yi musu adu ar fatan Alheri da Kuma Allah ya basu iKon gudanar da aiyukan cigaba da Kuma Samar da zaman lafiya a fadin kasan nan baki Daya. A karshe ya shawarci yan Najeriya da su baiwa Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shetima gohom baya a Koda yaushe domin su samu damar cika alkawiran da suka dauka a lokacin da suke gangamin Neman zabe.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie