Alhaji Muhammed Ibrahim 86 shine shugaban kungiyar Yan kasuwa na Arewacin Najeriya.....Alhaji Abdullahi.

Biyo bayan dambaruwan shugabanci ya wakana a cikin kungiyar yan kasuwar a rewacin Najeriya wanda hakan yasa shuwagaban nin kungiyar na jihohi shatara dake yankin na arewacin Najeriya ke nuna mubaya arsu ga shugaban kungiyar Alhaji Muhammed Ibrahim 86. Shuhaban kungiyar na shiyar jahar Taraba, kuma shugaban kwamitin zaben kungiyar ta kasa kana mataimakin shugaban kungiyar ta kasa shiyar arewa masau gabas Alhaji Abdullahi Usman yace ba abinda ya kowo haka illa san Bature da rashin sanin darajan shugabanci ne ya haifar da wannan matsala a cikin kungiyar. Alhaji Abdullahi Usman yace da can an tabayin makamacin haka ba a samu nasaraba to sun ganin in sunyi haka zasuyi nasara saboda haka garama su hakura domin bazasuyi nasaraba dalili kuwa shine a dokan kunguya Alhaji Muhammed Ibrahim 86 shine zababben shugaban kungiyar ta kasa. Ya kuma shaidawa wadanda kecewa sune shuwagabanin kungiyar su sanifa Shi Alhaji Muhammed Ibrahim 86, da Dan Bature tare da Kabiru Hali sune suka hadu suka assasa kungiyar karkaahin jagorancin Dan Bature. Bayan yayi murabus sai aka baiwa Alhaji Kabiru Hali riko lamarinda sukace bai iyaba aka karba aka baiwa Alhaji Ibrahim 86 riko to daganan sai aka gudanar da zabe wanda kuma Alhaji Ayuba yayi nasara kuma Alhaji Ibrahim yayi mass mubaya a. Hakan yasa ya zama mataimakin Alhaji Ayuba. Bayan antsar da Alhaji Ayuba aka fara cewa shidinma bai iyaban to daganan nefa sai aka kafa kwamitin shirya zabe wanda ninema na jagoranci kwamitin harma acikn wadana ke ikirarin cewa sune shuwagabanin kungiyar acikinsu akwai membobin kwamitin shirya zabe to ana cikin haka sai Allah yayiwa Alhaji Ayuba rasuwa, bayan anje anti gaisuwa rasuwar Alhaji Ayuba sai akace bai kamata a bar kungiyar ba shugababa wanda hakan yasa aka tabbatarwa Alhaji Muhammed Ibrahim 86 shugabancin kungiyar na kasa kuma kowa ya yarada ya amince. Alhaji Abdullahi ya kara da cewa a dokan kungiyar in aka zabi shugaba zaiyi was adadin shekaru hudune kuma a yanzu haka shekaru biyu yayi saboda haka ba wani shugaba kungiyar sai Alhaji Ibrahim 86. Da yake magana dangane da kwamitin amintattun da ake cewa sun rusa shugabanin kungiyar ta kasa to a dokan kungiyar kwamitin amintattu bai da hurimin rusa shuwagabanin ko nada shuwagabanin dolene sai an samu goyon bayan shuwagabanin kungiyar na jihohi sha tara da birnin tarayya Abuja san nan za a iya rusa ka nada shuwagabanin kungiyar a mataki na kasa. Saboda haka kwamitin amintattu shi kadai bazai rusa ko nada shuwagabanin kungiyar ba. Harwayau kwamitin amintattun bai da damar shirya zabe ko hana zabe dolene sai ya kira shuwagabanin kungiyar na jihohi ya tattauna dasu in sun amice to shikenan in kuma basu amiceba ta sa a hakura. Don haka Alhaji Muhammed Ibrahim 86 shine shugaban kungiyar yan kasuwa na arewacin Najeriya na kasa. Dangane da hadin kan yan kungiyar kuwa sai Alhaji Abdullahi yace kansu a hade yake domin in an duba yadda akayi zabe aka baiwa Alhaji Muhammed Ibrahim 86 hadin kai da goyon baya abun sha awane sosai, saboda haka sukam suna goyon bayan Alhaji Ibrahim 86 a matsayin shugaban kungiyar yan kasuwar arewacin Najeriya na kasa. Tare da kiran wadanda ke cewa sune shuwagabanin kungiyar na riko da suzo a hada kai domin ciyar da kungiyar gaba in kuma suna bukatar shugabanci ai sai su jira. Ya kuma yi Adu at Allah madaukakin sarki ya kawo cigaban kungiyar da zaman lafiya a tsakanin membobin kungiyar dama kasa baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie