Ana cigaba da baiyana cewa Alhaji Muhammed Ibrahim 86 shine halacceccen shugaban kungiyar Yan kasuwa Arewacin Najeriya.
A yayinda shuwagabanin kungiyar yan kasuwar arewacin Najeriya wadanda ke jihohi ke cigaba da nuna mubaya arsu ga shugaban kungiyar ta kasa Alhaji Muhammed Ibrahim 86. A matsayin shine halaccaccen shugaban kungiyar ta kasa.
Shugaban kungiyar yan kasuwar arewacin Najeriya shiyar jahar Yobe kuma mataimakin shugaban kungiyar na kasa. Alhaji Isa Adamu yace batun dambaruwan shugabanci dake faruwa a kungiyar son rai ne da kuma son shugabanci wanda wasu daga cikinmu keyi wanda kuma hakan ba zai haifar da da mai idoba.
Saboda haka wannan shugaba namu wato Alhaji Muhammed Ibrahim 86 shine halacceccen shugaba wanda dukkanin shuwagabanin kungiyar kama daga na kananan hukumomi, dana jihohi sha tara dake yankin arewacin Najeriya tare da birnin tarayya duk mun yarda da shi kum shine muka sani kuma shine aka zaba a matsayin shugaban kungiyar har na tsawon shekaru hudu.
Don haka inba son shugabanci da son zuciyaba tayaya wani haka kawai zai fito yace shine shugaba bayan kungiyar tana da zabeben shugaba kuma ma wa adinsa bai kareba, saboda haka wannan raina tsarin dokan Najeriya dana kungiyar. Don kan kungiyar a hade take sai dai wasu yan tsirarune daga cikinmu suke kokarin kawo rudani a cikin kungiyar wanda kuma baza suyi nasaraba da yardan Allah.
Alhaji Isa Adamu yace su sanifa kungiyar tana da dokokinta kuma akwai hanyoyi da akebi kafin mutum ya zama shugaba ba wai haka kawai mutum ya tashi yace shine shugaba saboda wasu mutane basu wuce gomaba sukace sun bashi shugabanci.saboda haka ankafa kungiyar ne akan dokoki don ba agun hirane aka kafataba.
Harwayau Alhaji Adamu yace ba yadda za ayi dubbain mutane sun zabi shugaban ace wai mutane biyar sun rusa abinda dubbain mutane sukayi ba zaiyuba. Kuma hankalima ba zaikamaba. Saboda haka mukam ba wanda mukasani a matsayin shugaban kungiyar yan kasuwa na yankin arewacin Najeriya sai Alhaji Muhammed Ibrahim 86.
Kuma duk mai son shugabanci sai ya hakura har sai Alhaji Ibrahim 86 ya kammala wa adinsa na shekaru hudu inda za a sake zabe kuma duk wanda Allah ya baiwa za a mara masa baya. Inma Alhaji Ibrahim dinne ya sake dawowa.
Saboda haka kungiyar a dunkule take wuri guda kuwa wasu kalilan baza su kawowa kungiyar cikasaban kuma bazasu hana ruwa guduba haarkokin kungiyar yana tafiya dai dai batare da wani fargababa.
Don haka idan anason hadin kai da cigaban kungiyar to a ksance anabin dokokin kungiyar sau da kafa domin akwai hanyoyi da akebi kafin a zama shugaba to dolene sai anbi hanyoyin in kuma baza abiba to ba za a samu cigaban kungiyar ba.
Amman a yanzu haka kam kashi can sa in da biyar zuwa da takwas na membobin kungiyar duk suna goyon bayan Alhaji Muhammed Ibrahim 86 domin shine aka zaba kuma aka yarda da shi a matsayin shugaban kungiyar.

Comments
Post a Comment