Hukumar Inshoran kiwon lafiya ta KASA shiyar jahar Adamawa ta day Alwashin ganin masu gajiyar Shirin kiwaon lafiya sun samu biyan bukatunsu.

Hukumar inshoran lafiya ta kasa ta bada tabbacin cewa daga yanzu masu cin gajiyar shirin a fadin kasa zasu samu saukin yadda ake basu kiwon lafiya. Jami'in kai komo na hukumar inshoran lafiya ta kasa dake jahar Adamawa, malam Abdulhakim Aliyu Musa ne ya bada wannan tabbacin yayin zaman kara wa juna sani karo na bakwai da masu ruwa da tsaki da ya wakana a birnin Yola fadar jahar Adamawa. Mallam Abdulhakim Aliyu Musa yace rattaba hannu kan kudirin dokar hukumar inshoran lafiya ta kasa wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tare da wannan sabon jadawalin gudanar da aiyuka na Wannan hukuma, za su kara mata karfi gurin tafiyar da al'amuran ta na samar da kiwon lafiya a fadin kasa. Jami'in kai komon yace akwai bukatar hukumar ta rika ganawa da masu cin gajiyar shirin inshoran lafiyar, wanda wani tsari ne da babban daraktan Hukumar na kasa ya kirkiro domin ji daga bakin al'umma kuma hakan zai taimaka wa hukumar gurin inganta aiyukan ta a fadin kasa. A cewar shi, sabon jadawalin gudanar da aiyukan zai maye gurbin tsohon kuma dukkan bayanan dake ciki daga mu'amala e hukumar na yau da kullum ne ta tattara su. Jami'in kai komon yace akwai kyakkyawar mu'amala tsakanin su da tsarin inshoran lafiya na jahar, tare da karin cewa akwai sauke sauke da dama a sabon jadawalin da zai rage yawan lokacin da ake dauka kafin samun umurnin tura mara lafiya wata cibiyar bada jinya dama sauran wasu matsalolin idan hakan ya taso. Da yayi jawabi kan sabon jadawalin aiyukan, Doctor Ibrahim Anas Usman na hukumar inshoran lafiya ta kasa yace akwai muhimman sauye sauye da dama da akayi a sabon kudirin dokar da shugaba Buhari yayi , hakan ne yasa hukumar ta sake nata jadawalin domin bata damar samun saukin aiyukan ta. Ibrahim Anas yace daga cikin dokar akwai na tabbatar da cewa duk wani dan Najeriya ko wanda yake Najeriya a hukumance ya shiga tsarin inshoran lafiyar. A cewar doctor Anas , idan dai ana son sabuwar dokar tayi tasiri, to dole ne sai an ɓullo da wannan jadawalin da zasu shawo kan kalubale da aka fuskanta a shekarun baya. Yace hukumar inshoran lafiya ta kasa ta shiga yarjejeniya da wasu kamfanonin hada magunguna da zasu rika yi mata magunguna domin kawar da zarge cewa magunguna basu da inganci. Haka shima da yayi jawabi kan hakkin masu cin gajiyar shirin, shugaban sashin shirye shirye na hukumar inshoran lafiya ta kasa da ke jahar Adamawa, Abubakar Lawal yace masu cin gajiyar shirin na da hakkoki da dama wa'danda suka hada dana sanin irin magunguna da za a basu da ma yadda akayi lissafin yadda za su biya kudaden magungunan da dai sauransu. Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki da suka halarci zaman sun bayyana yakinin su kan yadda hukumar inshoran lafiyar dake gudanar da aiyukan ta , tare da kira data kara sa ido kan asibitoci domin ganin an samu ingantaccen kiwon lafiya a fadin kasa. Kwanakwanan ne dai gwamnatin tarayya ta fitar da sabon jadawalin da zasu taimakawa kudirin dokar inshoran lafiya ta kasa a kokarin ta na ganin kowa yaci gajiyar shirin. Kuma yayin gabatar da jadawalin, ministan lafiya da kulawa da al'umma, Muhammad Pate, yace samun damar bada kiwon lafiya wa dukkanin bil'adama ne Mabudin cin ma burin tabbatar da kiwon lafiyar bai daya a fadin duniya.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie