Majalisar wakilain tarayya ta umurci ma aikatar aiyuka ta tarayya da ta binciki aikin gyaran hanyar Jibiro,sorou,Belel dake jahar Adamawa.
Majalisar wakilain tarayyar Najeriya ta baiwa ma aikatar aiyuka ta tarayya da tayi dukkanin mai yiwa domin dubawa da binciko dalilin da yasa har yanzu ba a kammal gyran hanyar Jibiro, Sorou , Belel dake jahar Adamawa hanya da ta hada Najeriya da janhueiyar Kamaru.
Tuninma majalisar ta kafa kwamitin da zai binciko lamarin na gyaran hanyar da aka bada kwangilarta akan nera biyon ashirin da shida. Wanda kuma tunin aka bayar da kudin.
Hakan ya biyo bayan da dan majalisar mai wakilta mazabar Fufore da Song a majalisar wakilain tarayyar Najeriya Wakili Boya ya tada batun a zaman majalisar.
Wakili Boya yace hanyar ya dauki tsawon shekaru bakwai ba tare da anwaiwayetaban duk da cewa an fitar da kudin kwangilan kuma hanyace da ake gudanar da hada hadan kaauwanci musammanma a tsakanin Najeriya da janhuriyar Kamaru.
Boya ya koka da yadda matuka motoci dama yan kasuwa keji a jika wajen gudanar da harkokinsu a yankin.
Wakili Boya wanda ahine shugaban kwamitin harkokin kwalejin ilimi ta tarayya a majalisar wakilain yace yana da muhimmanci a dauki matakin gaggawa domin ganin an kammala aikin gyran hanyar domin al umman yankin su samu damar gudanar da aiyukansu yadda ya kamata.
Ya kuma tabbatar da cewa zai yi dukkanin abinda suka dace domin ganin an samu moriyar damokiradiya dama cigaba a mazabarsa.

Comments
Post a Comment