Rundunan yan sandan Najeriya ta sanar da fara diban sabbin Jami anta.

Rudunan yan sandan Najeriya ta sanar da fara deban Jami an yan sandan ga duk wadanda sukayi nasaran a matsayin kurata a fannoni daban daban. A rana 15-10-2023 ne rundunan zata bude shafita na yanan gizo ga duk mai bukata zai iya cika takardan a yanan gizo wanda za a kwashe makwanni shida na cika takaradan wato daga ran 15-10-2023 zuwa ran 26-11-2023. Ga duk mai bukata zai ziyarci shafin rundunan a adreahi kamar hakahttp://apply.policerecruitment.gov.ng Kakakin rundunan yan sandan na kasa ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja kima aka rabawa manema labarai. Sanarwan ta baiyana cewa diban Jami an yan sandan yana daga cikin inganta aiyukan rundunan a wani matakin na inganta tsaro a fadin Najeriya. Sanarwan ta kara da cewa masu bakatan shiga aikin dan sandan ya kasance dan Najeriya, da kuma takardan shaidar kammala sakandare wato WAEC ko NECO wanda ke dauke da kiredi biyar wanda kuma an samu nasaran cin lissafi da harshen turanci. Kuma shekaru da ya kama daga 18 zuwa 25 ga wadanda zasu gudanar da aiyukan bai daya, a yayinda masu gudanar da aiyuka na musammànm kuma shekaunsu zaikasance daga 18 zuwa 28.sai kuma tsawon na miji kar ya gaza mita 1.67 na mata kuma mita 1.64 kuma yakasance ba a taba kama mutum da laifiba. Aiyuka na musamman din dai sun hada da kiwon lafiya al umma dana dabbobi, direba, tela, kafinta, walda, makaniki, da dai sauransu. Babban sifeton yan sandan Najeriya ya kirayi duk mai bukata shiga aikin dan sandan da yayi hattara da yan damfara ya kuma nuna farin cikinsa dangane da fara diban Jami an yan sandan ya kuma ja kunnen duk wanda wani mai aniyar damfara da yayiwa kansa kiyamun laili domin rundunan zata hukunta duk wanda tasa yana damfaran mutane.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie