An shawarci maniyata a jahar Gombe ya suyi kokarin kammala biyan kudin kujeran aikin Hajjin wannan shekara.

Babban sakataren hukumar Jin dadin da walwalan mahajjatan jahar Gombe Alhaji Sa adu Hassan ya shawarci maniyatan jahar Gombe da su Kara himma wajen biya kudaden kujerunsu domin ganin an samu damar gudanar da shirye shiryen da suka kamata akan lokaci Babban sakataren ya baiyana hakane a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake Gombe
Sa adu Hassan ya kirayi maniyatan da suyi iya kokarinsu da su kammala biyan kudin aikin Hajji na nera Milyon hudu da dubu Dari biyar akan lokaci domin kaucewa matsΓ loli. A cewarsa Hukumar aikin Hajji ta kasa NAHCON ta baiwa jahar ta Gombe kujeru dubu biyu da Dari biyar da shida a fadin jahar Wanda kawo yanzu sama da mutane dubu Daya sun kammala biyan kudadensu ga hukumar.
Sakataren ya yabawa shugabanci gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya Wanda ya jajirce wajen yin ruwa da tsaki domin ganin gudanar da aikin Hajji lafiya a Koda yaushe.
Hukumar ta bayyana cewa kudin aikin Hajjin wannan shekara ta 2024 baiyi tsada sosaiba.

Comments

Popular posts from this blog

π€πƒπ€πŒπ€π–π€ ππŽπ‹πˆπ‚π„ π‚πŽππ…πˆπ‘πŒ 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR π€π‚π‚πˆπƒπ„ππ“ πˆππ•πŽπ‹π•πˆππ† πŒπˆπ‹πˆπ“π€π‘π˜ π•π„π‡πˆπ‚π‹π„ 𝐀𝐍𝐃 π‚πŽπŒπŒπ„π‘π‚πˆπ€π‹ 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie