Dan takaran majalisar wakilain tarayyar Najeriya karkashin jam iyar ADC a mazabar Jalingo, Yerro, da Zing ya Sha alwashin samarwa matasa da mata aiki in har an zabeshi.
Daga Sani Yarina Jalingo
Dan takaran majalisar wakilain tarayyar Najeriya Mai wakiltar kananan hukumomi Jalingo, Yerro, da Kuma Zing daka jahar Taraba a karkashin jam iyar ADC Abdulrazaq Gidado yasha alwashin cirewa matasa kitse a wuta ta wajen Sama musu aikinyi mutukan aka zabeshi a zaben cike gurbi da za ayi a jahar.
Dan takaran ya baiyana hakane a zantawarsa da manema labarai a Jalingo fadar gwamnatin jahar ta Taraba.
Gidado ya dau alkawarin cewa indai har ya samu dama wakilta kananan hukumomin uku tofa mata da matasan yankin kayansu ya kunce a gidin kaba domin kuwa zaiyu iya kokarinsa na ganin ya samawa matasa da mata aiyukanyi domin dogara da kansu.
Yace tun a shekara ta 2014 Al ummar mazabarsa suka bukaci da ya tsaya takara a lokacin Yana manajan Darekta a hukumar yawon Bude ido don jakanema a wannan karo suka sake kiransa da yazo ya tsaya takaran Dan majalisar wakilain a zaben cika gurbi.
Gidado yace zaibi dukkanin dokokin tarayya domin ganin mazabarsa sunci moriyar daga gwamnatin tarayya, da suka hada da kiwon lafiya, Illimi, dama cigaban Al umma.
Ya Kuma jaddada aniyarsa na hada Kai da hukumomin tsaro walau na gwamnatin tarayya Dana jaha domin dakile kalubalen tsaro da ake ta fama dashi a yanzu. Ta taimaka musu da dukkanin abinda suka dace don su samu damar gudanar da aiyukansu yadda ya kamata.
Ya Kara da cewa ba zaije majalisar don yaji dadina zaijene domin kare miradun Al ummarsa ya kawo musu aiyukan cigaban yankin.
.
Hon Abdulrazaq Gidado (JAWAR) ya kirayi hukumar zabe maizaman kanta ta kasa INEC da ta tabbatar ta gudanar da zaben Mai inganci tare da shawartan abokan hamaiyarsa da subi kaidodi doka domin kaucewa taahin hankali.
Gidado ya Kuma kirayi Al umma kananan hukumomin Jalingo, Yerro, da Zing da su zabeshi a karkashin jam iyar ADC a ranan 3-2-2024 domin yayi alkawari bazaici amanarsuba.
Harwayau ya kirayi magoya nayansa da su kaucewa duk abinda zaikawo taahin hankali sudai su kare kuri unsu da za a Kai cibiyar tattara sakamokon zabe.




Comments
Post a Comment