Kungiyar Malamai Jami o I a Najeriya ASUU ta gudanar da bikin ranan gwarazaye..

Kungiyar Malamain Jami o I a Najeriya ASUU shiyar Jami ar Modibbo Adama dake Yola ta baiwa wasu membobinta dama wasu Mayan mutanae lambar yabo biyo bayan gudumawa da suka bayar na cigaba. Al umma da ma illimi. An dai bada Kyautar Yabon ne a dai dai lokacinda kungiyar ta ASUU ke gudanar da bikin ranan gwarzaye Wanda kungiyar ta saba gabatarwa a duk shekara Kuma bikin ya gudana ne a dakin taro na Jami ar Modibbo Adama dake nan Yola. Da yake gabatar da jawabi a wurin taron mataimakin shugaban Jami ar Modibbo Adama Farfesa Abdullahi Liman Tukur yace ya kamata a inganta Jami o I tare da Kiran malamain da sukasance masu hada kansu dayin aiki tukuru domin samun cigaban Jami o I dake fadin kasan nan.
Shima a jawabinsa shugaban taron Farfesa Abraham Okolo ya yabawa kungiyar ta ASUU bisa shirya irin wannan taron domin a cewarsa shirya taron makamacin haka zai karawa malamai kwarin gwiwar cigaba da gudanar da aiyukan cigaban Jami o I damq Al umma baki Daya. Shikuwa bako Mai jawabi Farfesa Lawan Garba Abubakar na Jami ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi ya gabatar da jawabinsa ne dangane da yadda kungiyar ta ASUU take jarjircewa wajen Neman hakki malamai da Kuma irin gwargarmaya da kungiyar keyi domin inganta karantarwar Jami o I a fadin Najeriya.
Saboda haka ya baiyana farin cikinsa dangane da lambar yabo da aka baiwa wasu da suka taka rawan gani waken taimakawa cigaba a bangarori daban daban. Tunda farko a jawabinsa na maraba shugaban kungiyar Malamain Jami o I shiyar Jami ar Modibbo Adama dake Yola Dr El Maude Jibrin ya baiyana farin cikinsa da godiyarsa ga mahalarta bikin wadanda suka fito daga sassa daban daban. Dr El Maude yace suna gudanar da irin wadannan bikine a kowace shekara domin dubawa da Kuma jinjinawa gwarazai wadanda suka jajirce wajen taimakawa Al umma. Don haka nema a wannan shekara aka baiwa wasu gwarazai lambar yabo tare da baiwa wasu dalube gurbin yin karatu kyauta domin su samu damar cigaba da karatunsu yadda ya kamata. Shima da yake nashi jawabi shugaban kungiyar Malamain Jami o I ASUU ta kasa Farfesa Emmanuel Victor Osodeke Shima jinjinawa kungiyar dama Jami ar Modibbo Adama yayi bisa shirya wannan biki na ranan gwarazai na wannan shekara. Wanda hakan zai karawa malamain kaimin cigaba da aiyukansu yadda ya kamata. Ya Kuma bukaci da gwamnati tayi tsaiwar daka wajen inganta Jami o I dama malamai domin hakan zai taimaka wajen cigaban illimi a fadin Najeriya. tare da Kiran daluben da sukasance suna baiwa kungiyar ta ASUU hadin Kai da goyon baya domin samun nasaran dama inganta karatunsu yadda ya kamata. .
Itama anata nagaren mataimakiyar gwamnan jahar Adamawa Farfesa Kaletapwa George Farauta yabawa tayi dangane da shirya wannan taro Wanda a cewarta hakan zaikawo cigaban illimi a cikin Jami o I. Mutane goma ne dai kungiyar ta baiwa lambar yabo da suka hada da Farfesa Kaletapwa Farauta, Farfesa Kyari Muhammed, da marigayiya Farfesa Jinti I Ndagana, Farfesa Kallamu Bulama, Farfesa Buba Aliyu Dr Adeniyi Oriolowo, Farfesa Chikezie I Owuama,Dr Abubakar Garba Iliya, Farfesa Hussaini Muhammed, Farfesa Mahmoud Jada. Harwayau Kungiyar ta baiwa dalube 13 gurbin yin karatu kyauta a Jami ar ta Modibbo Adama dake yola.biyo bayan kwazo da suka nuna a harkokin karatunsu. Da yake godiya a madadin wadanda suka samu Kyautar lambar yabon Dr Adeniyi ya baiyana farin cikinsa dangane da wannan girmanawa da akayi musu Wanda Kuma hakan zai basu kwarin gwiwa cigaba da aiyukan cigaban Al umma Kuma zasu cigaba da baiwa kungiyar ta ASUU hadin Kai da goyon baya domin samar da cigaban illimi. Suma daluben da suka samu gurbin karatun sun baiyana farin cikinsu da jindadinsu dangane da wannan taimaka da kungiyar ta ASUU ta basu Kuma a shirye suke su marawa kingiyar baya wajen fafutukan inganta Jami o I a Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie