Yan sanda a jahar Adamawa sun samu nasaran kashe mutane uku da ake zargi masu garkuwa da mutane ne tare da ceto mutane biyu da akayi garkuwa da su.

Rundunan yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran ceto mutane biyu tare da hallaka mutane uku da ake zargi masuyin garkuwa da mutane ne a tsaunin Koma daka wasu bangarorin kananan hukumomin Fufore da Jada a jahar Adamawa. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola. Sanarwan ta baiyana cewa rundunan karkashin rundunan dakile laifuka wato Crack tare da hadin gwiwar yan Kai, mafarauta, kungiyar Tabbital Pulaku inda sukayi diran mikiya a mabuyar masu garkuwa da mutane bayan sunyi dauki ba dadi da su ne dai hakan ya baiwa rundunan akawa da mutane uku kahira a yayinda wasu sun ranta ana kare da raunukan harbi a jikinsu, tare Kuma da ceto mutane biyu. Wadanda akayi garkuwa da su A rana karaba da ta gabata ne dai wasu dauke da makamai dira gidan Alhaji Jibo Karlahi inda sukayi awun gaba da Umar Jibo dan shejarau 18 da Hassan mai shekaru 13 zuwa nabayarsu Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya yabawa kwamnadan Crack da Jami ansa da kungiyar Tabitak Pulaku dama mafarauta bisa na mijin kokari da suakyi na dakile aikata kaifuka a fadin jahar. Kwamishinan ya Kuma kirayi daukacin Al ummar jahar ta Adamawa da sukasance suna taimakawa rundunan da wasu bayanai da zai taimakawa rundunan takawa masu tada zaune tsaye birki Ya Kuma tabbatarwa gwamnatin jahar dama Al ummar jahar Adamawa cewa rundunan ta kimtsa tsaf domin tarwatsa masu aukaya kaifuka daga maboyarsu dake fadin jaha rundunan ta kuma gano makamai a mabayar masu garkuwa da mutane tare da wasu kayaki.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie