Gwamnatin jahar Adamawa ta jinjinawa Rundunan Yan sandan jahar Adamawa.

 





Gwamnatin jahar Adamawa ta jinjinawa rundunan yan sandan jahar Adamawa bisa kokarinta na inganta tsaro a lokacin zanga zangan kasa da akayi.



Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.



Sanarwan tace a hunkunce gwamnatin jahar ta Adamawa ta yabawa rundunan yan sandan bisa nuna kwarewarsu  wajen gudanar da aiyukansu na kula da zanga zangan kasa Wanda hakan yasa ba a samu tashin hankaliba.



Da yake gabatar da takardan yabo a madadin gwamnatin jahar Adamawa mashawarci na musamman akan harkokin tsaro ga gwamna jahar Adamawa Hon. Ahmed Lawan ya jinjinawa rundunan Yan sanda bisa kokarinsa na maida hankali domin ganin an Samar da zaman lafiya da inganta tsaro kafin, da lokacin harma da bayan zanga zanga.




Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ya baiyana farin cikinsa da godiyarsa ga gwamna Umaru Fintiri  bisa wannan yabo da yayiwa rundunan, ya Kuma godewa Al umma jahar Adamawa bisa hadin Kai da suka baiwa rundunan yan sandan dama sauran hukumomin tsaro. Ya Kara da cewa kwarewa, hadinkai da taimakawa Al umma da mutunta hakkikin Al umma shine manyan aiyukan rundunan.




Kwamishinan ya Kuma yabawa dukkanin Jami an Yan sanda saboda jajircewa da sukayi na tabbatar da ganin an samu zaman lafiya da Kuma tsaro a tsakanin Al umma.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.