Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta Taya Al ummar musulmai jahar murnan bikin Maulidi.

 






Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Dankwambo Morris ya bukaci da a gudanar da bukuwar maulidi cikin kwanciyar hankali da lumana a fadin jahar Adamawa.



Kwamishinan ya baiyana haka ne a wata sanarwa da kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ya rabawa manema labarai a Yola.



Sanarwan ta baiyana cewa rundunan tunin ta baza Jami anta a sassa daban daban dake fadin jahar domin tabbatar da ganin an gudanar da bukuwar ba tsare da matsaloliba.



Don haka nema rundunan ke kira ga daukacin Al umma da sukasance masu baiwa hukumomin tsaro hadin Kai da goyon baya domin ganin an samu nasaran kare rayuka dama dukiyoyin Al umma.




Kwamishinan Yan sandan ya Kuma kirayi Al umma musulmai da suyi amfani da wannan lokacin na bikin Maulidi wajen yin adu o in wanzar da zaman lafiya a jahar tare Kuma da Kai rahoton dukkanin abinda basu amince da suna ga ofishin Yan sanda mafi kusa.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.