Rundunan NSCDC ta baiwa jami inta tukuncin kudi dubi 100.000. a jahar Adamawa.

 







Kwamanda rundunan tsaro bada kariya ga fararen hula a Najeriya NSCDC shiyar jahar Adamawa Idris Dahiru Bande ya kirayi jami an rundunan da sukasance suna gudanar da aiyukansu yadda ya kamata da Kuma bin doka tare da nuna da a domin cigaban rundunan a kasa baki Daya.





Kwamandan ya baiyana haka ne a lokacinda yake karawa Daya daga cikin Jami in rundunan wato Abubakar Abdulkadir mayos girma a shelkwatan rundunan dake sakatariya gwamnatin tarayya dake Yola.




Abubakar Abdulkadir mayos dai an karamasa girman ne sakamokon da ya tsnci jahar wata maniyaciya daga jahar Taraba Mai suna Maimuna Salihu dauke da kudin Amurka Dala Dari biyar da kudin Saudiya Dari uku kwatankwacin kudin Najeriya dubu dari takawa da hamsin 850.000. Wanda ya mayar mata jakanta.





Har wayau rundunan NSCDC  ta baiwa Abubakar Abdulkadir mayos tukunci kudi Naira 100.000.



Kwamanda Idris Bande ya shaida cewa Babban kwamanda Na kasa Ahmed Abubakar Audi ne ya amince da karawa mayos girma nan take wato daga mataimakin corsp na 11. Zuwa mataimakin Corsp 1.





Kwamanda ya Kuma shawarci Jami an da su Kara himma wajen gudanar da aiyukansu da Kuma gaskiya a Koda yaushe domin samun cigaban rundunan a kasa baki Daya.





Da yake jawabi Abubakar Abdulkadir mayos ya godewa rundunan bis Kara masa wannan girma Kuma abinda yayi na bayar da jaka Yana daga cikin aiyukan rundunan na kare maetaba da ma darajan Al umma.





Wakailain Hukumar aikin Hajji ta kasa karkashin jagorancin ko odinaron kula da aikin hajji na jihohin Adamawa da Taraba Ahmed Usman godiya ya yiwa rundunadan bisa wannan na mijin kokari da sukayi na karawa Jami in girma Wanda haka zai taikawa wajen karawa Jami an kwarin gwiwa wajen gudanar da aiyukansu yadda ya kamata,ta da Kiran saura hukumomin tsaro da Suma suyi koyi da rundunan ta NSCDC.




Shidai Abubakar Abdulkadir mayos Yana aiki ne da hukumar aikin hajji.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT