A CIGABA DA RIJISTAN KATIN ZABE AN BUKACI MATASA DA SUJE SUYI RIJISTA KATIN ZABE DOMIN SAMUN DAMAN ZABE A SHEKARA TA 2027.





Daga Alhassan Haladu Yola.




An shawarci matasa musammanma wadanda suka Kai right rijistan Katin zabe da sukaje ofishin hukumar zabe ko Kuma cibiyar da akeyin rijistan Kati da suyi rijistan Katin zabe Wanda hakan zai basu damar gudanar da zabe a Babban zaben shekara ta 2027.





Darectan Yan agajin kungiyar Izala Mai shelkwata a jos shiyar Jahar Adamawa Alhaji Ibrahim Usman Jalo ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a Yola.




Alhaji Ibrahim Jalo yace ya kamata Wanda suke da matsaloli a katinsu ko suka canja wurin da Suma karsuyi da wasa wajen zuwa ofishin hukumar zabe domin gyara katin zaben nasu.




A cewar Ibrahim Usman dai Katin zaben shi zai baiwa mutum damar shugaban da yakeso a zabe Mai zuwa saboda haka ya kamata matasa dama wadanda suke da matsala a katinsu da suyi dukkanin Mai yiwa domin tabbatar da ganin sun warware matsalarsu.




Ya Kuma kirayi jama a da sukasance masu hakuri da jimriya a Lokacin da suke yin rijistan domin samun nasara yin zaben shuwagabanin da suke so a zaben shekara ta 2027.




Ya shawarci hukumar zabe da itama ta Kara fadada cibiyoyin yin rijistan Katin zabe domin baiwa dukkanin Yan Najeriya da suka cancanci yin rijistan sun samu damar yin rijistan Katin zabe yadda ya kamata ba tare da matsalaba.




Kawo yanzu dai hukumar zabe Mai zaman kanta ta kasa na cigaba dayiwa Yan Najeriya rijistan Katin zabe a dukkanin ofishoshinta dake dukkanin kananan hukumomin 774 dake fadin Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT