AN BAIYANA IRIN AIYUKAN CIGABA DA GWAMNA FINTIRI YAYI A JAHAR ADAMAWA.
Daga Alhassan Haladu Yola.
An baiyana cewa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya gudanar da aiyukan cigaba a bangarori daban daban a fadin jahar Adamawa.
Mashawarci na musamman akan harkokin jama a ga gwamna Ahmadu Fintiri Barista Sunday Wugira ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola.
Barista Sunday Wugira yace gwamna Ahmadu Fintiri ya taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da aiyukan cigaban jahar Adamawa a bangarori daban daban da suka hada da ilimi, kiwon lafiya, harkokin noma, bunkasa harkokin kiwi, bunkasa kasiwanci, gyara hanyoyi, gine gine, da sauramsu a fadin jahar.
Barista Wugira yace a bangaren ilimi gwamna Fintiri ya gina makarantu zamani a dukkanin kananan hukumomin 21 dake fadin jahar Adamawa, ya Kuma Samar da kwalojoni daban daban a dukkanin shiyiyo uku dake fadin jahar tare da wadatar da dukkanin makarantu dake fadin jahar da kayakin koyarwarwa da na karatu domin bunkasa harkokin ilimi a fadin jahar baki Daya.
Harwayau gwamna ya taka rawan gani wajen diban malamai da dama wadanda suka fito daga dukkanin kananan hukumomi 21 dake fadin jahar a Wani mataki na inganta ilimi a fadin jahar, haka Kuma gwamna yayi kokarin wajen rage yawan yaran da basa zuwa makarantar Wanda hakan yasa akasaran Yara dake fadin jahar Adamawa suna zuwa makatarnta.
Barista Sunday yace a bangaren kiwon lafiya ma gwamna Fintiri ya Samar da manyan asibitici a kananan hukumomi tare da fadada wasu asbititcin, harma da Gina kananan asibitici a fadin jahar Wanda hakan ya taimaka wajen inganta harkokin kiwon lafiya a tsakanin Al umma dake fadin jahar.
Gwamna ya Kuma Debi ma aikatar kiwon lafiya dama likitoci tare da Samar da kayakin kiwon lafiya a dukkanin asibitici dake fadin jahar.
A bangaren tsaro ma gwamna Fintiri ya taka rawan gani domin ya wadatar da tsaro a dukkanin sassan dake fadin jahar Adamawa Wanda hakan ya taimaka wajen raguwar aikata laifuka da suka hada da sace sace kwace kwacen waya da dai sauramsu.
A bangaren ma aikatama yayi kokarin wajen inganta aiyukansu tare da diban ma aikata a bangarori daban daban Wanda hakan zai taimaka wajen rage rashin aikinyi a tsakanin matasa dake fadin jahar.
Gwamna yayi kakari wajen sanarwa matasa da mata aikinyi ta wajen koyar musu sana o I daban daban da Kuma tallafawa da jari ta Shirin rage talauci karkashin jagorancin PAWECA Wanda hakan ya taimaka wajen Samar da zaman lafiya a fadin jahar.
Sunday Wugira ya shawarci daukacin Al ummar jahar Adamawa da su kasance masu baiwa gwamnatin gwamna Fintiri hadin Kai da goyon baya domin ganin ya Samu nasaran cimma burinsa na gudanar da aiyukan cigaban jahar ta Adamawa baki Daya.

Comments
Post a Comment