FOMWAN TA YABAWA GWAMNA FINTIRI BISA KOKARINSA NA TALLAFAWA KUNGIYAR DA KAYAKIN ABINCI.

 











Daga Alhassan Haladu Yola.



Kungiyar musulmai mata a Najeriya  (FOMWAN), reshen Jihar Adamawa, ta bayyana matuƙar godiya ga Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, bisa gudummawar kayan abinci da ya bayar domin tallafa wa mambobinta a lokacin azumin watan Ramadan.



Kungiyar ta yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba gwamnan nasara a dukkan ayyukansa na alheri, tare da kare shi daga makiyansa.



Godiya ta biyo bayan bayar da buhuna 591 na kayan abinci da gwamnan ya yi, wanda suka hada da buhuna 525 na shinkafa da kuma buhuna 66 na sukari, domin sauƙaƙa gudanar da azumin watan Ramadan cikin kwanciyar hankali.




Da take zantawa da manema labarai a birnin Yola, Amira ta  FOMWAN a Jihar Adamawa, Hajiya Khadija Buba, ta bayyana wannan tallafi a matsayin abin a yaba da shi kuma yazo  a kan lokaci. Ta ce wannan taimako zai rage radadin halin ƙunci da iyalai da dama ke fuskanta a lokacin azumi.



Hajiya Khadija Buba ta sake miƙa godiya a madadin kungiyar, tare da roƙon Allah Ya saka wa gwamnan da alheri mai yawa bisa karamcinsa. Ta kuma tabbatar da cewa za a raba kayan tallafin cikin gaskiya da adalci domin su kai ga waɗanda suka cancanta ba tare da wata matsala

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.

ADAMAWA STATE POLICE COMMAND CELEBRATES WOMEN POLICE @ 70