An bukaci hadin Kai da zaman lafiya a tsakanin Al umma.
Daga Alhassan Haladu Yola.
An bukaci Al umma musulmai da sukasance masu hada kansu tare da taimakawa juna domin Samar da kyakkawar halaka da ma cigaban addinin musulunci yadda ya Kamata.
Shugaban majalisar harkokin addinin musulunci a jahar Adamawa Alhaji Gambo Jika ne yayi wannan Kira a lokacin da yake jawabi a wurin Buda baki Wanda kunguyar matasa musulmai a Najeriya Shiyar Jahar Adamawa ta shirya Wanda ya gudanar a sakatariya majalisar addinin musulunci dake Yola.
Alhaji Gambo Jika yace hadin Kai a tsakanin Al umma musulmai abune da yake da matukan muhimmanci don haka Yana da kyau Al umma musulmai sukasance masu yin dukkanin abinda suka dace domin Samar da hadin Kai a tsakanin Al umma musulmai.
Alhaji Gambo ya Kuma jaddada aniyar majalisar na baiwa dukkanin abinda zai kawo hadin Kai a tsakanin Al umma goyan baya domin ganin an Samu nasaran yadda ya Kamata.
Ya Kuma ja hankalin Al umma musulmai da su Kara himma wajen taimakawa marassa galihu musamman ma a wannan lokaci na Azumin watan Ramadan Wanda a cewarsa hakan Yana kawo hadin Kai a tsakanin Al umma.
Jika ya yabawa kungiyar matasa musulmai dangane da shirya wannan Buda bakai ga marassa galihu Wanda a cewarsa sunyi abin Azo a yaba, dafatan za sucigaba da wannan na mijin kokari da sukeyi.
Shima a jawabin sa na maraba shugaban kungiyar ta MUYAN a jahar Adamawa ENG. Musa Bello Modibbo yace sun shirya wannan Buda bakin ne saboda Samar da hadin Kai a tsakanin Al umma musulmai da Kuma zama Yan uwan juna kamar yadda Allah madaukakin sarki ya baiyana cewa mukasance Yan uwan juna kada mu rarraba. Saboda haka ne suka ya dace su shirya wannan Buda baki.
Shima a jawabinsa Alhaji Sani Jada yabawa yayi da wannan Buda baki da kungiyar MUYAN ta shirya, tare da ahawartansu da sucigaba da irin wadannan aiyuka domin Samar da hadin Kai a tsakanin Al umma.
Mai Hulda da jama a a kungiyara jahar Adamawa Abdullahi Njidda Damare ya jadda godiyarsu ga majalisar Addinin musulunci karkashin jagorancin Alhaji Gambo Jika da ta Basu wannan dama na shiraywa Al umma Buda baki,
A cewarsa majalisar ta taka rawan ganin wajen Basu goyon baya yadda yakamata Wanda Kuma haka ne ya kaisu ga Samun nasaran.
Buda bakin dai ya Samu jakartan jamma a da dama Wanda da suka fita daga sassa daban daban dake fadin jahar Adamawa.

Comments
Post a Comment