An bukaci iyaye su Maida hankali kan karatun yaransu domin ganin sun Samu inganceccen ilimi.

 







Daga Alhassan Haladu Yola.


 Wani mataki na inganta ilimi an kirayi iyaye a karamar Hukumar Yola ta rewa da sukasance masu Sanya Ido tare da tura yaransu makarnta Wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa ilimi a tsakanin dalube yadda ya Kamata.


Shugaban kwalejin Gen. Murtala Muhammed dake Yola Mallam Muhammed Alhaji Musa ne yayi wannan kira a lokacin da ya jagorancin rarrabawa dukkanin makarantu sakandare dake karamar Hukumar Yola ta arewa takardun karatu.



Mallam Muhammed Alhaji Musa yace tundra gwamnatin jahar karkashin jagorancin gwamna Ahmadu Fintiri ta taimaka da takarandun  karatu wa manyan makarantu sakandare, saboda haka ya Kamata iyaye Suma su Bada tasu gudumawa domin ganin yaran sun Samu inganceccen ilimi yadda ya Kamata.


A cewarsa iyaye su suke da Kaso Mafi tsoka wajen tura tare da Sanya Yara makaranta don haka ya Kamata iyaye suyi tunani sosai suka Kara Maida hankali wajen karatun yaransu domin ganin an Samu damar bunkasa ilimi a tsakanin yaran yadda ya Kamata.

 



Ya Kuma shawarci iyaye da malamai sukasance masu hada kansu a kid da yaushe Wanda hakan zai taimaka ganin yaran sun Samu inganceccen ilimi tare da Samun cigaba yadda ya Kamata.



Mallam Muhammed ya kirayi shuwagabanin makarantu da su tabbatar da cewa anyi anfani da takardun yadda yakamata ba tare da wata matsalaba, 



Mallam Muhammed ya Kara da cewa duk Wanda aka Samu da yin na dai daiba da takardun tofa zai fuskanci doka saboda haka kar suyi wasa ki sakaci da takardun .



Ya Kuma shawarci dalube da sukasance masu Maida hankali wajen karatunsu a Koda yaushe Wanda a cewarsa hakan zai taimaka musu wajen Samun nagarceccen ilimi da ya Kamata.



Suma malamain ya bukacesu da sukasance masu karantarwa bin hakki da gaskiya domin ganin yaran sun Samu damar cin jarabawan kammala sakandare wato waec da dai sauransu.



Ya Kuma yabawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa na mijin kokari da yake Yi na bunkasa harkokin ilimi da ma sauran aiyukan cigaban jahar da yake gudanarwa a bangarori daban daban dake jahar Adamawa.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.

ADAMAWA STATE POLICE COMMAND CELEBRATES WOMEN POLICE @ 70