KUNGIYAR MMPAN TA TAIMAKAWA MARAYU DA MARASSA GALIHU DA KUDADE A JAHAR ADAMAWA.

 





Daga Alhassan Haladu Yola.


Akalla marayu da marassa galihu da dama ne dai suka Samu taimako kudaden daga kungiyar musulmai ma aikatar kafafen yada labarai a Najeriya MMPAN Shiyar jahar Adamawa ta rarra musu jahar Adamawa.


Taron Bada taimakon ya gudana ne a sakatariyar kungiyar Jama atun Nasaril Islam dake cikin garin Jimeta a karamar Hukumar Yola ta arewa, Babban birnin jahar Adamawa.


Shugaban kungiyar ta MMPAN a jahar Adamawa Mallam Shehu Aliyu Wanda mataimakinsa Ibrahim Abubakar ya wakilta yace sun dauki matakin taimakawa marayu da marassa galihu ne duba da yada ake cikin watan Azumi Ramadan musamman ma a cikn kwani goma na karshen watan Ramadan.



Mallam Shehu yace aikata Alheri a cikin kwanaki goma na karshen watan Ramadan Yana da mutukan muhimmanci Wanda Kuma ana Samun Lada sosai son haka akwai bukatan Al umma musulmai sukasance masu taimakawa mabukata a Koda yaushe domin samu sakamoko mai kyau da Kuma cigaba.



Ibrahim Abubakar ya Kuma jadda da aniyar kungiyar na cigaban da Maida hankali wajen inganta rayuwar Al umma musammanma mabukata domin a cewarsa kungiyar ta gudanar da aiyukan inganta rayuwar Al umma dama cigaban Al umma ta fannoni daban daban.



 Ya Kuma baiyana cewa kungiyar ta gudanar da wannan aikin domin Nuna cewa Dan jaeida Yana da rawa da zai iya takawa wajen taimakawa Al umma a bangarori daban daban, saboda an sau a ranmbawa jamma a fiye da haka Amma saboda yanayi da ake ciki an Samu akasi.



Yayi Adu ar Allah ya karbi aiyukanmu yasa a kammla azumi lafiya Allah ya karbi dukkanin ibadun mu domin musamu tsira ranan gobe kiyama.


Da yake nashi jawabi shugaban majalisar harkokin musulunci a karamar Hukumar Yola ta arewa Alhaji Abdullahi Abubakar Butu ya yabawa kungiyar ta MMPAN bisa wannan jajircewa da sukayi ma Bada wannan taimaka Wanda sun gudanar da wannan taimako ne biyo jarajin da suka sanyawa kansu Wanda suka Tara wannan kudi da suka rabawa marayu da marassa galihu, Wanda Kuma hakan abune da ya dace.



Alhaji Abdullahi Butu ya kirayi sauran kungiyoyi da Suma suyi koyi da wannan kungiyar ta MMPAN ta wajen taimakawa mabukata a Koda yaushe.



Shima a nashi jawabi Alhaji Umar Bappari Kem Wanda ahugabane a kwamitin amintattu kungiyar ta MMPAN a jahar Adamawa, ya jaddada kiransa wajen aikata aiyukan Al heri acikin kwanaki goma na karshen watan Ramadan tare da Jin dadinsu da farin cikin dangane da wannan taimaka da kungiyar MMPAN tayiwa marayu da marassa galihu a fadin jahar Adamawa.



Alhaji Bappari ya yabawa kungiyar tare da Kiran Al umma da sukasance suna baiwa kungiyar ta MMPAN hadin Kai da goyon baya domin ganin sun cimma burinsu na taimakawa Al umma ba tare da wata matsalaba.


An dai baiwa marayu da marsa galihun kidade Wanda kowannensu ya Samu dubu biyar biyar, domin rage musu radadin dama taimaka musu saukin gudanar da azumi musammanma acikin kwanaki goma na karshen watan Ramadan.



Wasu da cikin wadanda suka Samu taimakon sun baiyana farin cikinsu da Jin dadinsu dangane da wannan taimako da akayi musu Wanda hakan ya Sanya musu farin ciki sosai tare da kian sauran kungiyoyi da Suma suyi koyi da kungiyar ta MMPAN wajen taimakawa mabukata a Koda yaushe.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins