MAJALISAR ADDININ MUSULUNCIN JAHAR ADAMAWA TA YANTA MUTUM SHIDA DAGA GIDAJEN YARI A JAHAR ADAMAWA.

 




Daga Alhassan Haladu Yola.



Majalisar Addinin Musulunci a jahar Adamawa ta yanta mazauna gidan yari shida tare da taimakawa da kayakin abinci was gidajen yarin uku dake cikin kananan hukumomi Yola ta arewa Yola ta kudu dake jahar Adamawa.


Majalisar ta yanta mazauna gidan yarin ne a zyara da ta Kai a gidajen yarin Jimeta dake karamar Hukumar Yola ta arewa, sai na Youlde Pate, da na Yola wadanda ke karamar Hukumar Yola ta kudu a jahar Adamawa.


Da yake yiwa mazauna gidan yarin jawabi shugaban majalisar Addinin musulunci Kuma shine ya jagoranci tawagan majalisar domin Kai ziyaran Mallam Gambo Jika yace sun kasance a gidajen yarin ne duba da yadda ake cikin kwanaki goma na karshen Ramadan Wanda a lokacin ne ake rubaiyya ibadu da Kuma aikata Alheri.


Saboda haka ne ma suka ga ya dace su kawo ziyara gidajen yarin tare da taimakawa da kayakin abinci, dama yanta wasu da cikin mazauna gidajen yarin.


Mallam Gambo ya Kuma shawarci mazauna gidajen yarin da sukasance masu canja halayensu da Kuma kaucewa dukkanin abinda zai kaisu ga shiga gidan yari.


Ya Kuma kirayesu da sukasance masu da a ga ma aikatan gidan yari  Wanda a cewarsa hakan ne zai basu damar zama lafiya da ma aikatan.

Jika ya kirayi mazauna gidan yarin da sukasance sun dogara ga Allah madaukakin sarki Kuma su kasance masu kiyaye duk abinda zai gurbata rayuwarsu Wanda hakan zai taimaka wajen Samar da rayuwa mai ingancin.


A  nasiha da ya gudanar Alhaji Umar Bappari Kem ya ja hankalin mazuna gidan yari da sukasance masu Maida komai ga Allah madaukakin sarki, da Kuma tuba a gareshi domin ganin sun Samu nasaran a rayuwa dama inganta rayuwarsu yadda ya Kamata.


Shima anashi jawabi mataimakin sakataren watsa labarai majalisar Muhammed Tukur yace kasancewarsu matasa ya Kamata a ce sun Maida hankali wajen inganta rayuwarsu ba wai sukasance masu aikata ashshaba.


Kwanturolan gidan yarin Yola ta kudu CSC Kassam ya godewa majalisar Addinin musulunci bisa wannan ziyara da taimako da suka kawo tare da tabbatar da cewa za ati amfani da abinda aka kawo ta hanyar da ta dace domin Samun cigaba.


Wasu daga cikin mazauna gidan yarin sun baiyana godiyarsu da Jin dadinsu dangane da yantasu da majalisar Addinin musulunci tayi tare da tabbatar da cewa baza su sake aikata laifukaba Kuma zasuyi iya kokarinsu domin ganin sun zama jakadu na gari.


Baya ga yanta mutane shida majalisar ta taimaka da kayakin abinci da suka hada da shinkafa, suga, magi, barguna, ga mazuna gidan yarin.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins