MUYAN ta rarrabawa marassa lafiya kayakin abinci a jahar Adamawa.




Daga Alhassan Haladu Yola 


Kungiyar matasa musulmai a Najeriya MUYAN Shiyar jahar Adamawa ta ziyarci Babban asibintin kwararru dake Yola domin taimaka musu da kayakin abinci a Wani mataki na Samun Lada dama tsira ranan gobe kiyama.


Ko odinatan rarraba kayakin Abdullahi Njidda Damare ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai Jin kadan bayan  rarrabawa marassa lafiya kayakin


Abdullahi Damare yace dalilin na kawo ziyara asibintin domin taimakawa marassa lafiya dai shine ganin yadda aka shiga kwanaki goma na karshen watan Ramadan Wanda a cewarsa kwanaki ne da suke da muhimmanci ga Al umma musulmai domin ana rubanya Lada aiyuka Alheri a wannan kwanaki goma.



Njidda Damare ya Kara da cewa zasu fadada aiyukansu zuwa wasu wurare daban daban da suka hada da gidajen yari, masallatai da dai sauransu.


Njidda ya Kuma baiyana cewa zasu fadada aiyukansu zuwa gidajen yari, masallatai dai sauransu domin ganin mutane da dama sun Samu Buda baki yadda ya Kamata.


Kungiyar ta MUYAN ta Kuma shirya Buda baki a Wani masallaci dake Anguwar NEPA domin Samar da hadin kan a tsakanin Al umma musulmai baki daya.


A cewar shugaban kunguyar ta MUYAN a jahar Adamawa Mallam Musa Bello Modibbo yace sun shirya wannan Buda baki ne domin Samar da hadin Kai da zaman lafiya a tsakanin Al umma musulmai, don ya Kamata al umma musulmai sukasance tsintsiya ma dairinki daya.kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ambata a cikin Al kur Ani mai girma.


Wasu daga cikin wadanda aka shiryawa Buda bakin dama marassa lafiya da aka ziyarta a asibiti sun baiyana godiyarsu da Jin dadinsu dangane da wannan taimako da aka kawo musu.


Cikin kayakin dai sun hada da abinci, lemo, da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.

TETFund Director Commends MAUTH Doctors Over Successful Separation of Conjoined Twins