An bukaci Al umma sukasance sun mallaki katin zabe domin zaban shuwagabanin da sukeso

 




Daga Alhassan Haladu Yola.


Domin  ganin an gudanar da Zabe cikin tsanaki da kwanciyar hankali an kirayi Al umma da sukasance sun mallaki katin zabe su Wanda hakan ne zai basu damar zaban shuwagabanin dake suke so a Babban zaɓen shekara ta 2927.


Mataimaki na musamman ga gwamna Ahmadu Finti kan harkokin jama a Barista Sunday Wugira ne ya Yi wannan Kira a zantawarsa da manema labarai a Yola.


Barista Sunday Wugira yace Yana da muhimmanci Al umma musammanma wadanda suka cancanci mallakar katin zabe da su gaggauta mallakar katin zabe domin shine zai basu damar zaban shugaban da zai cire masa kitse a wuta.



Wugira ya baiyana cewa an Dade ana gudanar da mulkin siyasa Amma cigaba da aka Samu Bai taka Kara ya karyaba, saboda haka Yana da muhimmanci Al umma suyi karatun ta nitsu wajen zaɓen shugaban da ya cancanci ya kagorancesu.



Barista ya shawarci masu zabe da kada su bari a rudesu ko a yaudaresu Kamata yayi su Maida hankali da taka tsan tsan wajen zakulo shuwagabanin da zasu shugabancesu na tare da wata matsalaba.



Sunday ya tabbatarwa Al umma cewa nifa suka bari Wani ya yaudaresu da Wani abinda ba zai kashe musu koshin ruwa ba suka zabeshi to su Sani kowa yaci kadan kuturu zai masa aski, saboda in sunga ba dai daiba kada su zargi kowa su zargi kansu.


Barista Sunday ya shawarci Al umma da kada su bari wasu su rudar dasu a fuskan addinin, ko banbancin siyasa, kabilanci, bangaranci, domin biyan bukatunsu, saboda haka Al umma suyi hattara da irin wadannan mutanen.



Ya Kuma baiyana cewa Al umma sukasance masu hada kan su a Koda yaushe da Kuma yiwa juna fatan Alheri tare da yin Adu o I Samar da zaman lafiya mai daurewa a tsakanin Jama a baki Daya.


Ya Kara da jan hankalin matasa da sukasance masu Bada gudumawa sosai wajen cigaban domokidiya da hadin Kai domin cigaban jahar dama kasa baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.