An bukaci mata musulmai da suyi rijista katin zabe da Kuma shiga kwamitin women in Da awa dake jahar Adamawa.

 







Daga Alhassan Haladu Yola.



An kirayi daukacon mata musulmai da su zo su shiga kwamitin women in Da awa domin gudanar da aiyukan cigaban addinin musulunci yadda ya Kamata.


Ko odinatan Kwamitin women in Da aw a jahar Adamawa Hajiya Rabi atu Ahmed Buhari ce tayi wannan Kira a zantawarta da manema labarai a Yola.


Hajiya Rabi atu Ahmed Buhari ta baiyana cewa akwai bukatar mata sukasance masu Bada gudumawa wajen Gina Addinin musulunci a Koda yaushe, saboda haka tana Kira da Babbar murya ga mata musulmai da su shugo cikin kwamitin women in Da awa domin Bada tasu gudumawa wajen cigaban addinin musulunci.



Hajiya Rabi atu Ahmed tace akwai aiyuka da dama Wanda ya Kamata ace mata musulmai sun Bada hadin Kai da goyon baya, Wanda hakan zai taimaka wajen cigaban addinin musulunci yadda ya Kamata.


Hajiya Rabi atu tace kawo yanzu suna gudanar da taro a kowace ranan lahadi na karshen wata a makarantar GRA dake daf da karantar FOMWAN, Saboda haka akwai bukatar mata suzo su shiga da Kuma karban Form din shiga a wajen Malama Rukayya.



Ko odinatan tace a yanzu haka kwamitin women in Da awa Yana da aiyuka da dama da yake gudanarwa don haka nema ake bukatan mata musulmai su shigo su Bada tasu gudumawa domin Samun nasaran cigaba.



A cewarta Kwamitin women in Da awa Yana gudanar da aiyuka da dama da suka hada da taimakawa marayu, hajiyayyu, masu bukata na musamman, da dai sauransu.


Ta Kuma jadda da aniyar kwamitin na cigaba da gudanar da aiyukan cigaban addinin musulunci a Koda yaushe.



Hajiya Rabi atu ta Kuma kirayi mata musamman wadanda basuyi rijistan katin zabe ba da su gaggauta zuwa ofishin Hukumar zabe domin yin rijista Wanda acewarta hakan ne zaisa su zabi shuwagabanin da sukeso a ranan zabe.


Hajiya ta baiyana cewa mata suna Bada muhimmiyar gudumawa wajen Zabe don haka Bai Kamata a barsu a bayaba su jajirce wajen ganin sun mallaki katin zabe su a hanu.


Ta Kuma shawarci mata musummanma wadanda suka cancanci yin rijista da suke suyi rijista, ga wadanda katinsu ya Samu matsala ko suka canja anguwa da suje su gyara domin su Samu damar gudanar da Zabe a shekara ta 2027.



Ta Kara da cewa mata sukasance masu hada kansu da Kuma jajircewa wajen aiyukan cigaban addinin domin Samun tsira ranan gobe kiyama.

Comments

Popular posts from this blog

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.