An bukaci mata sukasance masu Neman ilimi , su Kuma mallaki katin zabe.

 



Daga Alhassan Haladu Yola.



 ganin an bunkasa ilimi a tsakanin Al umma an kirayi mata da su Maida hankali wajen Neman ilimi  Wanda hakan zai taimaka wajen inganta ilimi a tsakanin Al umma baki Daya.


Amiran kungiyar Yan agaji na jama atu Nasaril Islam bangaren mata a jahar Adamawa Hajiya Amina Muhammed Bashir ce tayi wannan kira a zantawarta da manema labarai a Yola.



Hajiya Amina Muhammed tace ilimi ya mace Yana da matukan muhimmanci don haka Bai Kamata ayi sakaci da baiwa ya mace ilimiba, ya Kamata a inganta karatun yaran mata, domin a cewarsa baiwa ya mace ilimi kamar an ilimantar da duniyane.


Hajiya Amina  tace manzon Allah ya Bada umurni da a nemi ilimi Kuma Bai ware kowaba, saboda haka mata su Kara himma wajen Neman ilimi Wanda hakan zai basu damar karantar da yaramsu yadda ya Kamata.



Hajiya Amina ta Kuma baiyana cewa mata su sanifa sune suke tare da yara a Koda yaushe  don haka Neman ilimi wajibine domin ta ilimi ne zasu baiwa yaransu tarbiya  na gari da Kuma inganceccen ilimi.




Da wannan ne take kira ga iyaye da sukasance suna baiwa yaran mata ilimi a Koda yaushe kasancewa sune iyaye, saboda su Samu damar baiwa yaransu inganceccen tarbiya.




Hajiya Amina ta jaddada kiranta ga mata da sukasance masu rungumar koyon sana o I dama gudanar da kasiwanci domin a cewarta addinin musulunci Bai hanaba saboda haka mata suna da danar gudanar da kasiwanci yadda ya Kamata.




Ta Kara da shawartansu da su nisanta kansu ga duk abinda addini ya haramta domin kare martanarsu da Kuma tsira ranan gobe kiyama.




A cewarta mata suna da muhimmiyar gudumawa da zasu iya takawa wajen bunkasa ilimi a tsakanin Al umma don haka ya zama wajibi a baiwa mata ilimi da zai taimaka wajen inganta rayuwar Al umma.



Ta Kuma shawarci mata da su hanzarta zuwa karban katin zabe ko Kuma yin rijista Wanda hakan ne zai basu damar zaban shuwagabanin da suke so Wanda suke ganin zai cire musu kitse a wuta.

Comments

Popular posts from this blog

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.