AN NADA ALHAJI MUHAMMED ADAMU A MATSAYIN DAN MALIKI BATTA.
Daga Alhassan Haladu Yola.
Karamar Hukumar Demsa dake jahar Adamawa ta cika makil da Yan uwa da abokan Arziki wadanda suka fito daga sassa daban daban daga ciki da wajen Najeriya domin halartar bikin nadin Alhaji Muhammed Adamu Giwa a matsayin Dan Maliki batta, Wanda ya gudana a fadar Hamma Batta dake cikin karamar Hukumar Demsa.
Da yake nadish a matsayin Dan Maliki Batta, Hamma Batta, Homun Alhamdu Glastone Teneke yace ya nada Alhaji Muhammed Adamu a matsayin Dan Maliki Batta ne bisa cancantarsa da Kuma irin gudamawar da ya bayar wajen cigaban yankin Batta a bangarori daban daban da suka hada da tsaro, zaman lafiya, hadin Kai da dai sauransu.
Hamma Batta ya Kuma kirayi Alhaji Muhammed Adamu Dan Maliki Batta da ya cigaba da irin wannan namijin kokari da yakeyi na wanzar da zaman lafiya dama hadin kan jama a da Kuma baiwa masarautar hadin Kai da goyon baya domin Samun cigaban masarautar yadda ya Kamata.
A cewar Hamma Battan dai Alhaji Muhammed Adamu ta taka muhimmiyar rawa wajen Samun hadin Kai da zaman lafiya a yankin Batta dama kewaye baki Daya.
Da yake jawabi Jin kadan da nadashi a matsayin Dan Maliki Batta Alhaji Muhammed Adamu ya baiyana farin cikinsa dangane da nadashi Dan Maliki Batta, bayan ya godewa Allah madaukakin sarki ya godewa Hamma Batta bisa na dashi Dan Maliki Batta Wanda haka wata damace da Shima zai Bada nashi gudumawar wajen cigaban Yankin Bata a bangarori daban daban.
Alhaji Muhammed Adamu ya tabbatar da cewa da yardan Allah zaiyi dukkanin abinda suka dace domin cigaban masarautar dama yankin Batta baki Daya, da wannan nema yake kirayi ga daukacin Al umma yankin Batta da kewaye da sukasance masu hada kansu a Koda yaushe da Kuma baiwa masarautar Batta hadin Kai da goyon baya domin Samun cigaba yadda ya Kamata na tare da wata matsalaba.
Alhaji Muhammed Adamu yace abubuwa da dama sun burgeshi musammanma yadda jama suka ta tururuwa daga bangarori daban daban zuwa Demsa domin tayashi murnan nada shi Dan Maliki Batta, don haka Yana mai godewa dukkanin wadanda suka halarci bikin nadashi tare da yin Adu ar ga Allah ma daukakin sarki ya Maida kowa gidajensu lafiya.
Cikin wadanda suka halarci bikin wato Idris Modibbo Usman Tola sarkin maharbar yankin arewa masau gabas tare da Mustafa Ibrahim Al Amin ma taimakon shugaban kungiyar masu maganin gargajiya a yankin arewa masau gabas sun baiyana farin cikinsu da godiyarsu dangane da nada Alhaji Muhammed Adamu sarkin yaki a matsayin Dan Maliki Batta. Kuma a shirye suke su mara masa baya domin ganin ya Samu nasara.
Sun Kuma godewa Hamma Batta bisa baiwa Alhaji Muhammed Adamu a matsayin Dan Maliki Batta. Tare da Yi masa Adu ar Allah ya tayashi riko ya masa jagora.
An dai gudanar da liyafa da nishadi bayan nadin sarautar.

Comments
Post a Comment