Kungiyar Yusura Tasha Alwashin inganta rayuwar matasa a jahar Adamawa.
Daga Alhassan Haladu Yola.
A Wani mataki na inganta rayuwar matasa kungiyar Yusura da ya hada mata musulmai da matasa a Najeriya ta dukufa wajen cero matasa daga dukkanin abinda za bata rayuwarsu da mutincinsu da dai sauransu.
Amiran Kungiyar Yusura na mara Musulami da matasa a Najeriya Shiyar Jahar Adamawa Hajiya Maryam Rufa I ce ta baiyana haka a zantawarta da menema labarai a Yola.
Hajiya Maryam Rufa a I tace matasa sune kashin bayan kowace Al umma a fadin duniya saboda haka Bai Kamata ayi sakaci da kula da suba, kamata yayi a Kara kaimi wajen kula da rayuwarsu a Koda yaushe domin karesu daga shiga dabi u da Basu daceba.
Hajiya Maryam ta Kuma baiyana cewa kungiyar su ta Yusura da dukufa ka in da na in domin ganin matasa sun zama jakadu na gari a tsakanin Al umma domin wanzar da zaman lafiya mai daurewa.
Hajiya ta ce matasa sune kashin bayan kowace Al umma a fadin duniya, saboda haka nema kungiyarsu take shirya gangami a Koda yaushe domin wayarwa matasa Kai dangane da yadda zasu tafiyar da rayuwarsu yadda ta Kamata a tsakanin Al umma.
Ta Kuma kirayi matasa da su kaucewa dukkanin abinda zai kawar musu da hankali dama Wanda zai sasu suyi abinda bai kamataba, saboda haka tana jadddada kiranta ga matasan da sukasance masu koyon sana o I daban daban domin dogaro da kansu.
Amiran ta Kuma Kara da cewa kungiyarsu ta Yusura takan horar da matasa mata da Maza sana o I daban daban Wanda har gwamnati ta ma aikata koyar da kananan sana o I tana taimaka musu wajen horar da matasan.
Ta shawarci iyaye da sukasance masu ysayin daka kan tarbiyar yaransu a Koda yaushe su Kuma Maida hankali wajen shige da ficensu da kima sanin suwaye suke abokantaka da su, Wanda acewarta hakan zai taimaka wajen karesu daga fadawa banzan hali.
Har wayau Maryam ta shawarci mata da su maida hankali wajen Neman ilimin addini da na zamani domin a cewarta mara sune malimar Yara na farko saboda haka yana da muhimmanci mata su Kara kaimi wajen Neman ilimi a Koda yaushe.
Ta Kuma kirayi matasa da mata musamman wadanda suka cancanci yin rijistak katin zabe da suyi rijista katin zabe domin mallakar katin zaɓen shine yancinsu, tare da shawartansu da suje suyi rijistan katin shaidar Dan kasa.
Shima a jawabinsa shugaban bangaren matasa a kungiyar ta Yusura. Ahmed Bello Baba ya baiyana cewa suna wayarwa matasa Kai ta hanyoyi daban daban kuma suna Samun nasarori sasai a duk lokacinda suka shiryawa matasan gangami.
Ahmed Bello Baba yace saboda haka nema suka fadada aiyukansu zuwa ga dukkanin kananan hukumomi 21 dake fadin jahar Adamawa.
Ya Kuma Kara da cewa biyo bayan gangamin wayarwa matasan Kai sun Samu nasaran raguwar matasa wajen aikata harkan shaye shayen miyagun kwayoyi.
Saboda haka yake Kira ga daukacin Al umma dama iyaye da a madai hankali wajen janyo matasan a jiki da Kuma sanar da su illar shaye shaye a tsakanin Al umma. Domin Samar da cigaban zaman lafiya mai daurewa a tsakanin Jama a.

Comments
Post a Comment