Ma aikatar harkokin noma a jahar Adamawa ta dauki matakin dakile kalubale dake fuskantar manoma domin Samar da wadaceccen abinci.




Daga Alhassan Haladu Yola.



Ma aikatar harkokin noma a jahar Adamawa ta dauki matakin magance matsaloli da manoma ke fuskanta wadanda suka hada da rashin Samun inganceccen maganin feshi, dama iri da da dai sauransu.


Kwamishinan harkokin noma a jahar Adamawa Farfesa David Jatau ne ya baiyana haka a lokacin yake jawabi a wurin Taron tattaunawa da masu ruwa da tsaka akan harkokin noma dama hukumomin tsaro da ma sauran hukumomi Wanda ya gudanar a sakatariyar gwamnatin dake Yola.


Kwamishinan Wanda Babbar sakatariyar a ma aikatar harkokin noma a jahar Adamawa Mrs Heidi E Sunday ta wakilta tace sun taru da masu ruwa da tsaki ne wadanda suka hada da masu sayar da magunguna feshi, manoma, hukumomi, harma da jami an tsaro domin tattauna tare da hada Kai domin magance dukkanin kalubale da ake fuskanta a harkokin noma domin bunkasa tare da wadatar da abinci a fadin jahar.



Mrs Heidi Sunday ta kirayi masu sayar da kayakin amfanin noma da su tabbata sun Samu takardan izinin sayar da kayakin su daga hukumomin da dake da halaki kula dasu, kamar su NAFADC , Hukumar inganta iri a Najeriya da dai sauransu domin inganta aiyukansu ba tare da wata matsalaba.



Mrs Heidi tace hadin Kai a tsakanin ma aikatar da hukumomin dama manoma zai taimaka kwarai wajen bunkasa harkokin noma a fadin jahar Adamawa.



Tunda farko a jawabinsa na maraba Darectan aiyukan ma aikatar noma a jahar Adamawa Dr Ibrahim Bayaso ya baiyana cewa dalilinsu na na shirya wannan tattaunawa domin dubawa tare da zakulo hanyoyi da ya Kamata abi domin magance dukkanin matsaloli da ake fuskanta a harkokin noma a fadin jahar Adamawa.




Dr Ibrahim Bayaso ya jaddada kiransa ga masu sana ar sayar da kayakin noma da su tabbata sun Samu izinin sayar da kayakin daga hukumomin da lamarin ya rataya akansu Wanda acewarsa hakan ne zai basu damar sayar da kayakin su na tare da matsaloliba.



Dr Bayaso yace an dauki matakin hakane domin dakile matsaloli da ake Samu na yadda ake Samu rashin ingantattun kayakin noma ga manoma Wanda hakan ke haifar da koma baya a harkokin noma a fadin jahar Adamawa.



Ya Kuma shawarci manoma musammanma masu adama kayan abinci da sukasance masu yin taka tsan tsan wajen Adana kayan abinci da kada su sayarwa mutane kayakin abinci akwai sanadarin kashe kwari Wanda hakan zai yiwa jama a illa a lafiyarsu, don haka a kaucewa hakan.



Wasu daga cikin mahalarta Taron sun baiyana farin cikinsu dangane da shirya musu wannan taro da ta tabbatar da cewa zasuyi dukkanin abinda suka dace domin ganin an Samu nasaran inganta harkokin noma a fadin jahar Adamawa.



Sun Kuma tabbatar da Bada goyon bayansu dangane da aniyar gwamnatin dama ma aikatar harkokin noma domin Samar da wadaceccen abinci domin cigaban jahar ta Adamawa baki Daya.



Taron dai  ya Samu halartan hukumomin tsaro daban daban da Kuma hukumomi irinsu NAFDAC, na inganta iri a Najeriya, ma aikatu da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.