MAJALISAR ADDININ MISULUNCI A JAHAR ADAMAWA TA JAJINTAWA WADANDA HARIN GARIN GUYAKU YA SHAFA A KARAMAR HUKUMAR GOMBI.
Daga Alhassan Haladu Yola.
Majalisar harkokin addinin musulunci a jahar Adamawa da Mika ya aziyarta da jajenta ga wadanda harin Yan bindiga ya shafa a garin Guyaku dake cikin karamar Hukumar Gombi a jahar Adamawa.
Shugaban majalisar harkokin addinin musulunci a jahar Adamawa, Mallam Gambo Jika ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai a Yola.
Mallam Gambo Jika yayi Allah Wadai da Kai wannan hari inda ya baiyana shi da abin takaici ne tare da yin Adu ar Allah ma daukakin sarki ya kawo karshen matsalar baki Daya.
Mallam Gambo ya Mika ta azuyarsa ga iyalen wadanda suka rasa Yan uwansu da sarkin Gombi Kumu 1 na Gombi Agrey Bechor Ali da Kuma Alhaji Usman Ibrahim sarkin fada Guyaku, da ma daukacin Al ummar karamar Hukumar Gombi, bis wannan lanari da ya faru.
Ya Kuma Yi Adu ar Allah ya baiwa wadanda suka jikkata lafiya, Allah ya sa a gano wadanda suka Bata.
Ya Kuma kirayi hukumomin tsaro da su Kara kaimi wajen daukan matakai magance matsalar tsaro a fadin jahar dama kasa baki Daya.
Harin Yan bindiga dai yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata da dama a yayinda wasu Kuma suka Bata.

Comments
Post a Comment