MASU RUWA DA TSAKI DAKE CIKIN JIMETA SUN BUKACI ABBATI YA TSAYA DANTAKARAN SANATA.

 




Daga Alhassan Haladu Yola.


Al umma cikin garin Jimeta dama masu ruwa da tsaki sun bukaci da Aliyu AbdulHamid Wanda akafi Sani da Abbati da ya fito ya tsaya takaran Dan majalisar dattawa Wanda zai wakilci mazabar Adamawa ta tsaki a majalisar dattatwar Najeriya, a zaɓen shekara ta 2027.


Hakan na zuwane a Babban taro da Al ummar Jimeta suka gudanar Wanda ya Samu halartan dukkanin masu ruwa da tsaki dake cikin garin Jimeta.



Hon. Suleiman P A memba mai wakiltar karamar Hukumar Yola ta arewa a majalisar dokokin jahar Adamawa, ya baiyana farin cikinsa dangane da wannan taro musammanma kan bukatan Abbati ya tsaya takaran Santa, Wanda hakan abin farin ckine, saboda ya taka rawan gani a lokacin da yake rike da NISAL. don haka a shirye suke su mara masa baya domin ganin ya cimma nasara domin ceto Al ummar Jimeta.


Da yake gabatar da nashi jawabi Alhaji Isa Bagalci ya jaddada cewa Abbati ya gudanar da aiyukan cigaba a fannoni daban daban saboda haka ya zama wajibi su mara masa baya domin ya cigaba da aiyukan cigaba da yake da aniyar yi. Saboda haka Al ummar Jimeta na bukatarshi da ya tsaya takaran Sanata domin Samun cigaban Jimeta.


Shima a jawabinsa Hassan Turaki baiyana farin cikinsa yayi tare da cewa Daman Jimeta na bukatar irinsu Abbati, don haka muna Kira da Babbar murya ga Abbati da ya tsaya takaran Sanata domin cewa Al ummar Jimeta kitse daga wuta dama samawa matasa aikin Yi.


A cewar Hassan Turaki dai ba Wanda ya cancanci ya tsaya takaran Sanata a mazabar tsakiyar jahar Adamawa kamar Abbati.


Shi kuwa Kawu Wandala Kira yayi da a hada Kai domin acewarsa har yanzufa akwai wadanda basa Bada hadin Kai don haka ya zama wajibi Al umma Jimeta sukasance masu hada kansu a key da yaushe domin hakan ne zai kaisu ga Samu cigaba, ya Kuma jaddada aniyarasa na baiwa Abbati goyon baya wajen tsayawarsa Sanata.



Shima Danjuma iliyasu yace su mazauna garin Jimeta suna goyon bayan Abbati Dari bisa Dari dangane da tsayawarsa takaran Sanata saboda haka Al ummar Jimeta na bukatarshi da ya tsaya takaran Sanata Wanda zai wakilci mazabar Adamawa da tsakiyar a majalisar dattatwar Najeriya.



Da yake nashi jawabi Aliyu AbdulHamid ya baiyana cewa ya Kamata ace Jimeta ta Mori romon domokiradiya domin a cewarsa akwai abubuwa da dama da Jimeta Bata Samu, don haka in har ya Samu nasara zai kawo abubuwar more rayuwa daban daban, ya Kuma baiyana farin cikinsa da Jin dadinsa dangane da goyon baya da aka bashi Kuma da yardan Allah ba zai baiwa mararda kunyaba.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.