Gwamnatin jahar Adamawa ta Debi malamai 5000 a fadin jahar.

 






Daga Alhassan Haladu Yola.



 Wani mataki na inganta ilimi a fadin jahar Adamawa hakan yasa aka kirayi malamai da sukasance masu hada kai da iyaye tare da gudanar da aiyukansu bisa tsoron Allah da Kuma bilhakki da gaskiya.


Babban sakataren Hukumar dake kula da makarantu gaba da firamare dake jahar Adamawa Mr Birsan Penuel ne ya Yi wannan Kira a lokacinda ake baiwa sabbin malamai takardan shaidar daukan aiki a shelkwtan Hukumar dake Yola.


Mr Birsan Penuel  yace daukan sabbin malamai 5000 da gwamnati jahar Adamawa tayi zai taimaka wajen coke gibi da ake dashi na bukatar malamai a fadin jahar ta Adamawa.


Mr Birsan ya yabawa gwamnatin jahar Adamawa karkashin jagorancin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa kokarinsa na inganta fanning illimi, Wanda a cewarsa gwamna Fintiri ya taimaka ya taka rawan gani wajen cigaban ilimi a fadin jahar Adamawa.


Mr Penuel yace tunda yazo Hukumar ta PPSMB. Hukumar dake kula da makarantu gaba da firamare a jahar Adamawa ta Samu nasarori sosai wajen gudanar da  aiyukan cigaban ilimi a dukkanin makarantu gaba da firamare a bangarori daban daban, wadanda suka hada  da rarraba litattafai, daban daban a dukkanin makarantu sakandare dake fadin jahar.



Mr Birsan Penuel ya baiyana cewa kawo yanzu dukkanin makarantu sakandare kimiya sun Samu kayakin gwaje gwaje da littafain kimiya daban daban da dai sauransu.


Ya Kuma tabbatar da cewa Hukumar zata cigaba da yin dukkanin abinda suka dace domin Samun cigaban illimi a fadin jahar ta Adamawa.


Ya shawarci iyaye da su kasance masu baiwa malamai da Hukumar hadin Kai da goyon baya domin ganin dalibe sun Samu inganceccen illimi yadda ya Kamata.


A cewar Mr Penuel yace iyaye suna da rawa da zasu iya takawa wajen inganta karatun Yara , kasancewa yaran suna zama da iyaye na sa o I 16 a yayinda sa o I sama da 7 ne suke makarantar, saboda haka ya Kamata iyaye su taimaka domin ganin yaran sun Samu inganceccen ilimi.


Ya shawarci iyaye da sukasance suna baiwa gwamnatin karkaahin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri goyon baya da hadin Kai domin ganin ya Samu nasaran bunkasa harkokin illimi a fadin jahar Adamawa.


Birsan ya Kuma kirayi dalube da su Maida hankali wajen karatunsu da Kuma zuwa makarantar akan lokaci da Kuma biyayya ga malamai dama shuwagabanin domin Samun albarkacin karatunsu.

Comments

Popular posts from this blog

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.