Monday Simon ya kai ziyarar neman albarka a daga sarakunan Shelleng da Guyuk
Daga Alhassan Haladu Yola.
Duban magoya bayan dan takaran kujerar majalisar Tarayya a mazabar Guyuk da Shelleng Hon Monday Simon ya kai ziyarar neman albarka da addu'ar samun Nasara daga sarkunan Shelleng da Guyuk
Yayin da tawagar ta isa garin Shelleng, magoya bayan jam’iyyar da mazauna yankin sun tarbe shi da kaɗe-kaɗe da raye-raye tare da bayyana aniyarsu ta mara masa baya domin samun nasara a zaɓe zai zuwa.
Dan takarar kujerar majalisar Tarayya a mazabar Guyuk da Shelleng, ya gabatar da fom ɗin tsayawa takararsa tare da neman albarka da addu’o’in samun nasara a zaɓe mai zuwa.
Hakazalika, tawagar tasa ta wuce zuwa Guyuk, inda ya kai ziyara fadar Kwandi Nunguraya Kurhaye, Dishong Dan Sanda na Biyu, domin gabatar da fom ɗinsa da kuma neman goyon baya.
Da yake jawabi yayin rangadin, Monday Simon ya yi alƙawarin samar da wakilci nagari mai adalci, shugabanci na kusa da jama’a, da kuma buɗaɗɗiyar gwamnati idan aka zaɓe shi ya wakilci mazabar Guyuk da Shelleng a Majalisar Tarayya.
Monday Simon ya Kuma tabbatar da cewa idan an bashi dama ya zama Dan majalisar tarayya zai samarwa matasa da mata aiyukan dogaro da Kai harma da Samar da gurbin karatu domin inganta ilimi a yankin baki Daya.
Saboda haka matasa da mata sukasance masu hada kansu su Kuma bashi goyon baya domin Samar da cigaba da ma zaman lafiya mai daurewa a yankin dama jaha ba


Comments
Post a Comment